Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-07 18:59:12    
An mai da hankali kan nauyin karatu fiye da kima da ke bisa wuyan 'yan makarantu na kasar Sin

cri

Yanzu kasar Sin tana yin kokari wajen daga matsayin ayyukan koyarwa, amma lokacin da ake tafiyar da wannan aiki, wani batu ya jawo hakulan mutane sosai, wato a birane da garuruwan kasar Sin, musamman ma a manyan biranen kasar, nauyin karatu da ke bisa wuyan yara yana da yawa fiye da kima. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da iyaye da dimbin yawa suna bukatar yaransu wajen samun lacca iri daban daban daga malamai bayan aji domin neman samun karuwa a fannoni da yawa. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wata yarinya mai shekaru 7 da haihuwa wadda ake kiranta Junjun, mu ji abubuwan farin ciki da bakin ciki da take gamuwa lokacin da take koyon fasahar yin wasa da kayan kida.

Wannan rana Lahadi ce, amma tun sassafe, Junjun ta fara goge Erhu. Erhu shi ne wani kayan kida na gargajiya na kasar Sin, kuma a kan kiransa Viollin na kasar Sin. Mahaifin Junjun shi ne wani direban taksi, kuma mahaifiyarta ita ce wata mai sayar da kayayyaki a kanti, kuma kakanninta suna gida bayan da suka yi ritaya. Junjun ta gaya mana cewa, ba ta taba hutawa a lokacin huhu ba. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da dole ne ta je gidan malaminta don koyon fasahar goge Erhu a cikin kwanaki biyu na hutu. Bayan da ta yi kalaci, ta kan bar gida tare da kakanta. Kuma kakan Junjun ya gaya mana cewa, "Lalle mun tilasta wa Junjun wajen koyon fasahar goge Erhu a lokacin da ta fara koyonsa, daga baya kuma mun gano cewa, koyon fasahar yin wasa da kayan kida zai ba da taimako gare ta wajen kyautata basira, yanzu ta iya yin tilawa sosai daga hadda."

Kamar yadda kakan Junjun ya fada, koyon fasahar yin wasa da kayan kida yana iya taimaka wa yara wajen kyautata bisara. Amma a hakika dai, abu mafi muhimmanci shi ne iyaye suna fatan yaransu za su iya samun fasahohi da yawa idan an kwatanta su da sauran yara, ta yadda za a iya taimaka masu wajen samun fifiko kan shiga makarantu masu inganci. Alal misali, domin shiga jami'a, Junjun ta fara ayyukan share fage a shekarunta ya kai 3 da haihuwa.

Ban da koyon Erhu, Junjun ita ma ta shiga kwasa-kwasan horaswa wajen rutubu da Turanci da ilmin lissafi da dai sauransu. Ko da yake nufin iyalanta yana da kyau, amma Junjun ta ji gajiya sosai wajen karatu. Kuma ta gaya mana cewa, "Ina jin gajiya sosai wajen koyon fasahar goge Erhu. Ba na iya hutawa ko kadan ba a lokacin hutu. A ran asabar da kuma ran lahadi, na kan shiga kwasa-kwasan horaswa iri daban daban."

A hakika dai, akwai irin wadannan yara kamar Junjun masu dimbin yawa a biranen kasar Sin. Bisa kidayar da aka bayar, an ce, fiye da rabin yara da ke birane sun taba ko kuma suna koyon fasahar yin wasa da kayayyakin kida. Haka kuma a lokacin hutu, a kalla rabi daga cikinsu su kan samu lacca iri daban daban daga malamai bayan aji.

Amma namijin kokarin da Junjun ta yi bai iya ba ta tabbaci wajen shiga wata makaranta mai inganci sosai ba. Ban da samun lacca iri daban daban daga malamai bayan aji, domin Junjun ta iya shiga wata muhimmiyar makaranta mai inganci sosai ta birnin Beijing, iyayenta suna bukatar biyan kudade masu yawa. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da iyaye masu yawa suna fatan yaransu za su iya shiga makarantu masu inganci sosai, shi ya sa sun biya kudade masu yawa ga makarantun da suke so domin neman samun izin shigowa.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, iyaye suna bukatar kashe kudade fiye da kudin Sin yuan dubu 200 wajen horar da wani dan makarantar sakandare. Kudi yuan dubu 200 shi ne dukkan albashin da mahaifiyar Junjun ta samu a cikin shekaru fiye da goma. Sabo da haka warware batun zabar makaranta ya zama wani muhimmin abu ne wajen rage nauyin kudi da ke bisa iyayen yara wajen karatu.

Zhou Ji, ministan ilmi na kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, "A shekarar da ta gabata, kasar Sin ta fitar da sabuwar dokar ba da ilmin tilas, inda aka tanada cewa, 'yan makaranta da suke cikin matakin ba da ilmin tilas na shekaru 9 suna iya shiga makarantun da ke kusa da gidajensu ba tare da yin jarrabawa ba. Wannan ya shaida cewa, ba za a amince da zabar makarantu ba, kuma ba za a amince da karbar kudade ba kamar yadda ya kamata ba."

Amma wani hani kawai ba ya iya kau da burin iyaye wajen samar da wata makoma mai kyau ga yaransu. Game da wannan Mr. Zhou ya bayyana cewa, ya nuna fahimta sosai ga irin wannan burin iyaye, shi ya sa lokacin da ake hana zabar makaranta, kasar Sin tana kyautata yanayin karatu da kuma ingancin ayyukan koyarwa na makarantu, ta yadda iyaye da yaransu ba za su nuna damuwa ga makarantu ba. (Kande Gao)