Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-04 20:25:39    
Kasashen Sin da Rasha ke kokori wajen kyautata tsarin cinikayyarsu

cri

Bayan da aka kaddamar da bikin shekara na kasar Sin da ake shiryawa a kasar Rasha a watan Maris da ya wuce, sai nan da nan masu masana'antu na kasashen biyu suka rattaba hannu a kan yarjejeniyoyi 21 game da hadin kansu a fannin tattalin arziki da cinikayya wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 4.3. Wannan ya alamanta cewa, kasashen biyu sun shiga cikin wani sabon lokaci na inganta hadin kansu cikin sauri a fannin tattalin arziki da cinikayya.

A shekarar bara, yawan kudi da aka samu daga wajen cinikayyar da aka yi a tsakanin kasashen Sin da Rasha ya kai dalar Amurka biliyan 33.4, wato ke nan ya karu da kashi 14.7 cikin dari bisa na shekarar 2005. A yayin da shugabannin kasashen biyu ke bayyana farin cikinsu ga sakamako mai kyau da kasashen biyu ke samu wajen hadin kan tattalin arziki da cinikayya, kuma suna mai da hankali sosai ga matsaloli da aka gamu da su wajen yin cinikayya a tsakanin kasashen biyu.

Malam Zhang Zhonghua, kwarare a cibiyar nazarin al'amuran yau da kullum ta kasar Sin yana ganin cewa, yanzu, babbar matsala da ake fuskanta a fannin tsarin cikikayya tsakanin kasashen Sin da Rasha, ita ce tsarin cinikayyar ya shafi wani bangare kawai, musamman na'urori masu aiki da wutar lantarki da suke cinikayyarsu sun yi kadan. Ya ce, "yawan na'urori masu aiki da wutar lantarki da kasar Rasha ke fitarwa zuwa kasar Sin yana ta raguwa sannu a hankali. Dangane da matsalolin da ake fuskanta wajen hadin kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Rasha, kasar Sin tana so ta yi kokari sosai wajen kyautata tsarin cinikayya a tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a daga matsayin hadin kan kasashen biyu sosai a fannin tatttalin arziki da cinikayya."

Gwamnatin kasar Sin ta shirya wani babban nunin kasar Sin a birnin Moscow ne, musamman domin kyautata tsarin cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Rasha. A lokacin nunin, daruruwan masana'antun kasar Sin sun je kasar Rasha, inda suka kulla yarjejeniyoyi da dama a tsakaninsu da masana'antun Rasha dangane da shigowa da na'urori masu aiki da wutar lantarki daga kasar Rasha wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 500.

Putin, shugaban kasar Rasha ya nuna yabo ga bukukuwan shekarar Sin ciki har da babban nunin kasar da ake shiryawa a kasar Rasha. Ya ce, "makasudin shirya irin wadannan manyan bukukuwa kamar haka shi ne domin ingantawa da kara daga matsayin hadin kai a tsakanin kasashenmu biyu. Ta hanyar yin harkokin tattalin arziki da cinikayya da al'adu, za a kara sa kaimi ga harkoki da jama'ar kasashen biyu ke yi a tsakaninsu. Sa

'an nan kuma za a sami taimako daga wajensu ta yadda jama'armu za su kara fahimtar juna, da ba da tabbaci ga kiyaye kyakkyawar dangantaka a tsakanin kasashenmu biyu."

Kwararrun sun nuna cewa, daidaita tsarin cinikayya a tsakanin Sin da Rasha wani babban aiki ne na dogon lokaci. Malam Zhang Zhonghua yana ganin cewa, "yanzu, kasar Sin tana gudanar da tsarin tattalin arziki na kasuwanni. Sabo da haka gwamnatin kasar ba za ta iya tilastawa msana'antu da su yi irin wannan hadin giuwa ba, sai ta iya nuna musu jogaranci ko sa musu kaimi wajen yin hadin guiwar. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, kasar Rasha ta yi kokari sosai wajen daga matsayin sana'ar kera na'urorinsu, don kara kwarewa wajen yin takara a kasuwanni."

Bayan haka malam Zhang ya kara da cewa, ba ma kawai kasashen Sin da Rasha suna hadin guiwarsu a fannin na'urori masu aiki da wutar lantarki ba, har ma ya kamata su inganta hadin kansu wajen zuba jari da kimiyya da fasaha, yayin da suke kokarin kyautata tsarin cinikayya da ake yi a tsakanin kasashen biyu. Yanzu a hakika dai, gwamnatocin kasashen biyu sun riga sun fara daukar matakai daban daban don neman kyautata tsarin nan. (Halilu)