Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-04 20:11:07    
Ziyarar gani da ido a filaye da dakunan wasannin Olympic (1)

cri

Aminai Afrikawa, ko kuna sane da ,cewa gagarumin taron wasannin Olympic na Baijing yana kusantowa . Zuwa karshen shekarar da muke ciki, za a kammala aikin gina dukan filaye da dakuna guda 37 da ake bukata domin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Wadannan filaye da dakuna, kowanensu yana da nasa sigar musamman, wanda kuma muke iya gabatar muku da wani labari mai ban sha'awa a gare shi. To, tun daga shirinmu na yau, za mu dan gutsura muku labarai a game da wadannan filaye da dakuna. Ina fatan za ku ji dadin saurarensu.

Yau, bari in karanta muku wani labari game da filin wasan kwallo mai laushi wato softball na Fengtai, wanda za a yi amfani da shi a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Wannan ne filin wasannin Olympic na farko na Beijing da aka kammala gina shi da kuma fara aiki da shi.

Filin wasan softball na Fengtai yana kudancin birnin Beijing. An soma gina shi ne a ran 28 ga watan Yuli na shekarar 2005. Fadin filin ya kai murabba'in mita kimanin 15,000. Wannan filin wasa yana da tabatattun kujeru 4,700 da kuma kujeru na wucin gadi 5,000, inda ake iya daukar 'yan kallo da yawansu ya zarce 13,000. An kammala aikin gina shi ne a watan Yuli na shekarar da ta gabata.

Jim kadan bayan an kammala aikin gina shi, sai nan da nan aka gudanar da gasar cin kofin duniya ta 11 ta wasan softball na mata. Wannan ne karo na farko da aka gudanar da gasar jarrabawa ta taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 a nan yankin Beijing. A lokacin da ake gudanar da wannan gasa, hadaddiyar kungiyar wasan softball ta kasa da kasa,da 'yan wasa mahalartan gasar, da masu koyar da 'yan wasa da kuma alkalan wasa dukansu sun yi yabo sosai ga kyakkyawan ingancin filin wasan. Mr.Don Porter, shugaban hadaddiyar kungiyar wasan softball ta kasa da kasa ya sha fadin, cewa "kila filin wasan softball na Fengtai, wani filin wasa ne mafi kyau a tarihin wasan softball. Ya kuma yi fatan za a mayar da filin wasan softball na Fengtai a matsayin cibiyar horar da 'yan wasan softball ta Asiya.

Domin gina wani filin wasannin Olympic na zamani, masu gina filin na Fengtai sun sanya kokari matuka.

Ana bukatar kyakkyawan ingancin kasa mai launinja da ake kira ' Red Soil' a Turance domin shimfida su a doron kasa na wurin kai hari da aka kebe a cikin filin wasan softball. Siffar filin wasan softball tana kama da na maficici mai kusurwa uku. Ban da karamin wurin kai hari tsakanin 'yan wasa da aka kebe cikin filin wasan, kuma akwai wurin musamman da aka kebe, inda aka shimfida ciyayi a doron kasa. Saboda 'yan wasa sukan yi gudu kan filin wasan, don haka dole ne a shimfida kasa mai launin ja maras kauri a doron kasa na filin,wadda take kama da rairayi idan an taba su. Sashen da abun ya shafa na unguwar Fengtai yan kashe kudin kasar Sin wato Renminbi Yuan miliyan biyu don sayo su daga kudancin kasar Sin. Amma, idan ana so a gudanar da gasa a hukumance, to wajibi ne za a shigo da kasa mai launin ja daga kasashen waje.

Ko da yake an kashe kudade masu yawan gaske wajen gina filin wasan softball na Fengtai, amma duk da haka, an yi tsimi gwargwadon iyaka wajen gina shi. Alal misali: an yi amfani da fitilu masu tsimin makamashi da kuma batir dake da makamashin da aka samo daga hasken rana domin samar da ruwan zafi ga filin wasan. Ban da wannan kuma, masu yin kasafin filin wasan sun bi akidar kirkire-kirkire, wato ke nan sun harhada na'urorin tsamo ruwa masu karfin gaske a karkashin dodon kasa na filin wasa na ciyayi domin magance tattarar ruwan sama.

Harkokin dashen itatuwa da kyawawan furanni da na zirga-zirga a kewayen filin wasan softball na Fengtai, ana gudanar da su bisa ma'aunin kasa da kasa. Labuddah wannan ya samu karbuwa sosai daga mazaunan birnin Beijing.

Jama'a masu saurare, lallai ba a manta ba, a lokacin da ake gudanar da gagarumar gasar cin kofin duniya ta wasan softball na mata a watan Agusta na shekarar da ta gabata, kwamitin shirya gasar ta gudanar da yunkurin fadakar da kan bainal jama'a a fannin wasan softball ba tare da bata lokaci ba; ban da wannan kuma ya rage yawan kudin tikitin shiga domin samar da dama ga mazaunan birnin masu tarin yawa su yi kallon wasan. Ga alamun ba za a damu da shan wahalar sayen tikitocin kallo ba. ( Sani Wang )