Ran 2 ga wata, Mr. Mohamed Ali al-Mardi ministan shri'a na kasar Sudan ya sanar da cewa, gwamnatin kasar Sudan ba ta amince da umurnin da kotun kasa da kasa mai kula da manyan laifuffuka ta bayar na kame mutane 2 na kasar wadanda ake zargi da aikata laifukan yaki a yankin Darfur".
Mr. al-Mardi ya ce, kasar Sudan ba ta rattaba hannu a "dokar Rome" ba wadda ta kafa kotun kasa da kasa mai kula da manyan laifuffuka, shi ya sa, wannan kotun ba ta da ikon yin hukunci ga mutanen kasar Sudan. Ya ce, umurnin kame wadannan mutane da kotun ta bayar yana da "alaka da siyasa", nufinsa shi ne matsa lamba ga gwamnatin kasar Sudan.
Ran 2 ga wata, kotun kasa da kasa mai kula da manyan laifuffuka da ke Hague na kasar Holland ta bayar da sanarwar, inda ta sanar da cewa, a ran 27 ga watan Afrilu, alkali na wannan kotun ya riga ya ba da umurnin kame Ahmed Haroun babban tsohon jami'in ma'aikatar harkokin gida da Ali Kushayb jagoran dakarun yankin Darfur na kasar Sudan, saboda ba shakka suna da hannu a laifukan yaki da cin zarafin 'yan Adam a yankin Darfur. Wannan ne karo na farko da kotun kasa da kasa mai kula da manyan laifuffuka ta ba da umurnin kame ga mutanen da aka zargi da laifin yakin Darfur.
|