Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-02 21:06:26    
Kafuwar babban zauren cibiyoyin nazari na Confucius daga shafinmu na internet

cri
Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Husseinistan Lawal Yakubu, wanda ya zo daga birnin Kano da ke tarayyar Nijeriya. Kwanan baya, bayan da ya sami wani labari dangane da kafuwar babban zauren cibiyoyin nazari na Confucius daga shafinmu na internet, sai ya turo mana wata wasika da cewa, yaushe ne za a kafa cibiyar Confucius a Nijeriya, domin zai taimaka ma irinmu da ke da ra'ayin Sinanci da kuma kasar Sin da ma al'amuran da suka shafe ta. To, watakila akwai masu sauraron da ba su da wata masaniya dangane da cibiyar nan ta nazari ta Confucius, sabo da haka, za mu yi takaitaccen bayani a kan cibiyar tare kuma da amsa tambayar malam Husseinistan Lawal Yakubu.

A yayin da Sin ta cimma dimbin nasarori a wajen bude kofarta ga kasashen duniya, harshe da al'adu na kara taka muhimmiyar rawa a wajen cudanyar da ke tsakaninta da kasashe daban daban. A hannu daya kuma, kasashen duniya suna kara sha'awar koyon Sinanci da fahimtar kasar Sin. A cikin irin wannan hali ne, Sin ta yi koyi da yadda sauran kasashe suka yi, ta ba da shawarar kafa cibiyoyin Confucius a wasu kasashe, don biyan bukatun jama'a a fannin koyon Sinanci da kuma gudanar da harkokin musanyar al'adu, ta yadda Sin za ta iya bayar da gudummowarta ta fuskar raya duniya mai jituwa. Sabo da haka, a watan Nuwamba na shekarar 2004, Sin ta bude cibiyar Confucius ta farko a kasar Koriya ta kudu.

Cibiyar Confucius hukumar ilmantarwa ce da Sin ta kafa tare da hadin gwiwar kasashen waje, kuma manufarta ita ce kara fahimtar da jama'ar duniya dangane da harshen kasar Sin da kuma al'adunta, da bunkasa huldar aminci da ke tsakanin Sin da kasashen waje da kuma sa kaimi ga bunkasuwar al'adu iri daban daban na duniya, ta yadda Sin za ta iya bayar da nata taimako wajen raya duniya mai jituwa. Nauyin da ke bisa wuyan cibiyoyin Confucius shi ne koyar da Sinanci da kuma gudanar da mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen waje a fannonin ilmantarwa da al'adu da tattalin arziki da sauransu, ciki har da koyar wa mutanen bangarori daban daban Sinanci da horar da malaman koyar da Sinanci da gudanar da jarrabawar Sinanci da tabbatar wa malamai iznin koyar da Sinanci. Bayan haka, suna kuma samar da labaran da suke shafar ilmantarwa da al'adu da tattalin arziki da zaman al'umma na kasar Sin da kuma gudanar da nazari a kan kasar Sin ta zamani.

Tun bayan da aka kafa cibiyar Confucius ta farko a kasar Koriya ta kudu a shekarar 2004, sai cibiyoyin confucius suka yi ta bunkasa cikin sauri. Ya zuwa yanzu, Sin ta rigaya ta kafa cibiyoyin Confucius fiye da 140 a kasashe da shiyyoyin duniya sama da 50. A Afirka ma, ana ta kara sha'awar Sinanci da kuma al'adun kasar Sin. A watan Disamba na shekarar 2005, an bude cibiyar Confucius a kasar Kenya, wadda ta kasance ta farko da aka kafa a nahiyar Afirka. Daga bisani, sai cibiyoyin sun yi ta yaduwa a nahiyar, ya zuwa yanzu dai, an riga an bude cibiyoyin Confucius guda 9 a kasashen Afirka, wadanda suke kasashen Kenya da Masar da Zimbabuwe da Ruwanda da Afirka ta kudu da Nijeriya da kuma Madagascar. A yanzu haka a Nijeriya, an bude cibiyoyin Confucius biyu, wato daya a jami'ar Nnamdi Azikiwe wadda aka bude a ran 15 ga watan Faburairu na shekarar da muke ciki, wadda ta kasance cibiyar confucius ta farko da aka kafa a kasar, dayan kuma aka kafa ta a jami'ar Lagos.

Kafuwar wadannan cibiyoyin Confucius a kasashe daban daban sun jawo martani sosai daga kasashen, kamar yadda jaridar NewYork Times ta yi sharhin cewa, "cibiyoyin Confucius sun daukaka amanar kasar Sin da kuma kwantar da hankulan sauran kasashe dangane da wannan kasa mai matukar girma." Haka ne, ko da yake kasancewar cibiyoyin Confucius hukumomin nazarin harshe da kuma al'adu, amma kafuwarsu ta kara fadakar da jama'ar kasashe daban daban kan harshen kasar Sin da al'adunta da kuma zaman al'ummarta, kuma sun kara karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da kasashe daban daban, har ma sun sami karbuwa sosai a daga kasashe daban daban.

Malam Husseinistan Lawal da dai sauran masu sauraron da ke sha'awar Sinanci da al'adun Sin, muna kuma muku maraba da zuwa cibiyoyin Confucius, don kara fahimtar harshen Sin da ma al'adunta.(Lubabatu)