Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-02 21:05:09    
Kasar Sin tana kiyaye littattafan tarihi na zamanin aru-aru daga dukkan fannoni

cri

Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, za ta soma wani aikin binciken littattafan tarihi na zamanin aru-aru a cikin shekaru biyar masu zuwa don samun labari dangane da yawan littattafan tarihi na zamanin aru-aru da ke kasancewa da darajarsu da halin da suke ciki wajen tanadinsu da kuma bayar da littafin rubuta sunayen wadannan littattafai da horar da kwararrun gyara littattafai, har da yin amfani da Injuna masu kwakwalwa wajen aiwatar da harkokin aiki don kara karfafa ayyukan kiyaye littattafan tarihi na zamanin aru-aru.

Kasar Sin tana da tarihin rubuce-rubuce da yawan shekarunsa ya kai dubu 4 ko fiye. A zamanin aru-aru na kasar Sin, ban da kalmomin da aka rubuta a kan takardu , sai akwai kalmomin da aka rubuta a kan gora da siliki, abin da muka ce a kan littattafan tarihi na zamanin aru-aru shi ne littattafan tarihin da aka rubuta kalmomi a kan takardu, a gun wannan binciken da ake yi kan littattafan tarihi na zamanin aru-aru, za a bincike littattafan tarihi iri daban daban da aka rubuta ta hanyar yin amfani da kalmomin kabilar Han da na sauran kananan kabilu kafin shekarar 1912. kuma ana tanadinsu ne a cikin gidajen ajiye littattafai da gidajen baje koli da sauran hukumomi, wasu ma ana tanadinsu a tsakanin jama'a. Bisa kimantawar da kwararru suka yi, an ce, yawansu ya wuce miliyan 30. A cikin tarihi na dogon lokaci, wasunsu an lalata su bisa sakamakon hargitsin yake-yake, wasu kuma kwari sun lalata su, saboda haka bai kamata ba a bata lokaci wajen kiyaye wadannan littattafai.

A gun wannan bincike, sassan da abin ya shafa na kasar Sin sun bayar da ma'aunoni iri iri da yawa a jere, kuma sun gabatar da bukatu wajen gina sito-siton ajiye littattafan tarihi na zamanin aru-aru da yin amfani da fasahohin gyara su. Wata jami'a mai kula da aikin gina gidajen ajiye littattafan tarihi ta ma'aikatar al'adu ta kasar Sin malama Liu Xiaoqin ta bayyana cewa, wurare daban daban na kasar Sin sun sami bambanci sosai a tsakaninsu wajen samun sharadin tanadin littattafan, dalilin da ya sa haka shi ne saboda ba a tsara ma'auni da bukatu irin bai daya a da ba, wajen yin aiki mai kyau da na maras kyau , an sami rata sosai a tsakaninsu , wato wajen aiki mai kyau, ana iya kiyaye wadannan littattafai cikin zafin da ba a canja ba, tare kuma daukar matakan kiyaye daidaicin ruwa da hana cizon kwari da datti da dai sauransu, amma wajen aikin maras kyau da aka yi, ana ajiye littattafan a kan kanta na ajiye littattafai yadda aka ga dama.

Malama Liu Xiaoqin ta bayyana cewa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta ware kudadden musamman wajen kiyaye littattafan bisa matakai daban daban, za a mai da hankali sosai ga kuyaye littattafan da ke da daraja sosai.

Wani kwararren gyara littattafan tarihi na zamanin aru-aur na kasar Sin mai suna Du Wei ya bayyana cewa, dole ne matakin da aka dauka zai dace da halin da ake ciki na tanadin littattafan tarihi na zamanin aru-aru sosai da sosai, kuma an gabatar da sabbin bukatu na maganin gurbata iska da kiyaye muhallin tanadinsu. Wajen gyara su, ya kamata a dauki matakin zamani sosai don tanada su cikin dogon lokaci.

Yanzu a kasar Sin, an sami kwararrun gyara littattafan tarihi na zamanin aru-aru da yawansu ya kai 100 kawai, kuma yawancinsu ba a yi musu horo sosai da sosai ba, fasaharsu da suka gada daga malamansu kawai, ana bukatar sauyawar fasaharsu wajen gyara littattafan da tsarin ilminsu.

Saboda haka, an riga an tsara shirin mayar da aikin horar da kwararru cikin ayyukan da za a yi da gaggawa . Shugaban wani gidan ajiye litattafai na kasa mai suna Zhang Ping ya bayyana cewa, ayyuka mafiya muhimmanci gare mu wajen horar da kwararru guda biyu ne, na daya, tsai da matakan kiyaye littattafan, na biyu, tabbatar da fasahar da ma'aikatanmu na yanzu suke rikewa tare kuma horar da sabbin ma'aikata.(Halima)