Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-02 20:52:07    
Shahararriyar 'yar wasan kasar Sin ta samar da almara a tarihin wasan tsunduma cikin ruwa

cri

A gun gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya da aka kammala a birnin Melbourne na kasar Australia ba da jimawa ba, 'yar wasa Guo Jingjing ta kasar Sin ta zama zakara a cikin gasar tsunduma cikin ruwa daga katako mai tsayin mita 3 da ta tsakanin mata biyu biyu a lokaci guda, ta haka ta zama 'yar wasa ta farko a tarihin gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya, saboda ta zama zakara har sau 4 a jere a cikin gasanni 2 iri daya, ta samar da wata almara a tarihin wannan muhimmiyar gasa.

Har kullum kungiyar wasan tsunduma cikin ruwa ta kasar Sin tana gwada gwanintarta sosai a rukunin wasan iyo na duniya, an mayar da ita a matsayin kungiyar da ake mata zaton nasara, Guo Jingjing kuwa ta fi nagarta a cikin wannan kungiya mai karfi. Wannan budurwa mai shekaru 26 da haihuwa ta sami lambobin zinariya da yawa a cikin dukkan taron wasannin Olympic da gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya.

A cikin karon karshe na gasar tsunduma cikin ruwa daga katako mai tsayin mita 3 a tsakanin mata, 'yan kallo sun cika zauren cibiyar wasan kan ruwa ta Melbourne, dubban masu kishin iyo na kasar Sin sun yi sowa domin karfafa gwiwar Guo Jingjing. Tun daga farkon gasar har zuwa karshe, Guo Jingjing ta yi ta zama ta farko, a karshe dai ta zama zakara, ta zama 'yar wasa ta farko a tarihin gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya saboda ta sami lambar zinariya har sau 4 a jere a cikin wata gasa.

Bayan gasar, a cikin natsuwa ne Guo Jingjing ta yi bayani kan zama zakara sau 4 a jere a cikin gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya, ta ce, 'Ko wace lambar zinariya da na samu a gun gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya tana da matukar muhimmanci a gare ni.'

A cikin gasar tsunduma cikin ruwa daga katako mai matsayin mita 3 a tsakanin mata biyu biyu a lokaci guda, Guo Jingjing da abokiyar kungiyarta Wu Minxia ba su gamu da kalubale ko kadan ba, sun zama zakara a karshe dai. Sun fi samun maki fiye da 37 bisa 'yan wasan kasar Jamus, wadanda suka zama na biyu.

Guo Jingjin ta taba samun lambobin zinariya 8 da na azurfa 1 a cikin gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya sau 5, a birnin Melbourne, ta ci nasara mai muhimmanci a ranta na wasan tsunduma cikin ruwa, amma karo na karshe ke nan da ta shiga wannan muhimmiyar gasar duniya, saboda za ta yi ritaya bayan taron wasannin Olympic na Beijing. Bayan gasar, a maimakon jin bakin ciki saboda ba ta ci gaba da shiga gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya ba, Guo Jingjing ta yi sakin jiki da kuma farin ciki saboda samun cikakiyyar nasara a cikin gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya sau 5.

Taron wasannin Olympic sau 3 da gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya sau 5 da yin horo har na tsawon shekaru fiye da 20 (a cikin filin wasan tsunduma cikin ruwa )da kuma jin farin ciki da bakin ciki sau da yawa da ba a iya kidaya yawansu ba, a idon Guo Jingjing, abubuwan da suka karfafa gwiwarta wajen yin kokari har zuwa yanzu su ne yin hakuri da kuma tashi tsaye. Ta ce, 'Saboda na yi shekaru da yawa ina samun horo, na kan gamu da matsaloli daban daban a mataki daban daban, in na tashi tsaye, in jure wahala, to zan ji sakin jiki. Ni tsohuwa ce a kungiyarmu, na yi shekaru 20 ina samun horo, ko da yake a ganin saura, ban sha wahala a gun gasanni ba, kuma ina da karfi sosai, amma a gaskiya na yi namijin kokari a lokacin horo, shi ya sa na kan ji gajiya, a wani lokaci ina son in daina saboda matukar gajiya, amma a lokacin can, ya zama wajibi ne in tashi tsaye, idan na daina, mai yiwuwa ne ba zan sami ci gaba ba.'

A yayin da aka nemi shawo kanta da ta ci gaba da ranta na wasan tsunduma cikin ruwa, Guo Jingjing ta ce, ta gamsu da nasarorin da ta samu a gun gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya sau 5, ba za ta nemi zama zakara har sau 5 a jere a wannan gasa ba, taron wasannin Olympic na Beijing da za a yi a shekara mai zuwa dandamali ne na karshe a gare ta a fannin wasan tsunduma cikin ruwa. Game da yin ritaya, Guo ta yi bayanin cewa,'Dalilin da ya sa na yi ritaya shi ne domin lokaci ya yi. A cikin rukunin wasan tsunduma cikin ruwa na kasar Sin, ni ce tsohuwa, a da ko kusa babu wanda ya ci gaba da yin takara a lokacin da yake da shekaru 26 da haihuwa kamar ni.'

Yanzu mutane na sa fatan alheri domin ganin murmushin da Guo Jingjing za ta yi a gun taron wasannin Olympic na Beijing na shakarar 2008, irin wannan murmushi zai ci gaba da kasancewa har abada bayan shekarar 2008.