Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-02 20:49:46    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(26/04-02/05)

cri
Ran 26 ga watan Afirl, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kaddamar da kasafin wutar yola ta taron wasannin Olympic na Beijing da kuma hanyar da za a bi wajen bai wa juna wannan wutar yola. An yi zanen wannan wutar yola ne bisa tunanin 'asali daya da yin zaman tare cikin jituwa'. Tsayin wannan wutar yola ya kai centimeter 72, nauyinta ya kai gram 985. Sa'an nan kuma, kwamitin ya yi karin bayani kan hanyar da aka tsara domin bai wa juna wutar yola. An mayar da 'ziyara ta sada jituwa' tamkar taken harkar bai wa juna wutar yola ta taron wasannin Olympic na Beijing. Wutar Yola za ta tashi daga nan Beijing, hedkwatar kasar Sin a ran 31 ga watan Maris na shekara ta 2008, za ta ratsa birane 22 a ketare da kuma birane da yankuna 113 a gida, za ta dawo babban filin wasa a ran 8 ga watan Agusta na shekara mai zuwa, inda za a yi bikin bude taron wasannin Olympic na Beijing. Za a yi kwanaki 130 ana mika wa juna wutar yola har na tsawon kilomita dubu 137. Kazalika kuma wutar yola za ta kai kololuwar tsaunin Everest, wadda ita ce tsauni mafi tsayi a duk duniya.

A 'yan kwanakin nan da suka wuce, an riga an soma dasa tsire-tsire a damshin kasa da ke kudancin wurin shakatawa na gandun daji na wasan Olympic na Beijing. An yi shirin dasa tsire-tsire ire-ire 10 ko fiye a nan, yawan tsire-tsiren zai wuce dubu 500. Bisa shirin da aka tsara, za kammala dasa dukkan tsire-tsire iri daban daban a wannan damshin kasa a karshen watan Mayu na wannan shekara.

Ran 28 ga watan Afril, an fara aiki da sabuwar tashar internet ta taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na duniya na shekara ta 2007 cikin Sinanci da Turanci da Faransanci da Rashanci da Larabci da kuma harshen Spain a hukunce. An sami wannan sabuwar tashar internet wato www.2007specialolympics.com ne bayan da aka kyautata tsohuwar tashar internet ta fuskar tsare-tsare da abubuwan da ke cikin tashar internet da kuma amfaninta, ita dandali ne kawai da taron wasannin Olympic na musamman ya ba da labarunsa.

Kwanan baya, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon badminton ta kasa da kasa wato IBF ta gabatar da sabuwar takardar jerin sunayen 'yan wasan kwallon badminton na duniya, inda 'yan wasan kasar Sin suka ci gaba da zama na farko wajen gasar tsakanin namiji da namiji da ta tsakanin mace da mace da ta tsakanin maza biyu biyu da ta tsakanin mata biyu biyu.(Tasallah)