Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-02 18:26:05    
shugaba Bush na Amurka ya yi watsi da shirin doka da majalisun dokoki na kasar suka gabata kan ware kudi domin yaki

cri

Ran 1 ga wata, a hukunce ne shugaba George W. Bush na kasar Amurka ya yi watsi da shirin doka da majalisun dokoki na Amurka suka bayar kan ware kudi domin yaki, ta haka rikicin da ke tsakanin fadar gwamantin Amurka wato White House da majalisun dokoki na Amurka game da batun ware kudi domin yaki ya kara tsananta. Amma masu nazarin harkokin yau da kullum suna ganin cewa, jam'iyyar Dimokuradiyya da ta Republican za su yi sassauci kadan a fannin tsara sabon shiri kan ware kudi domin yaki, ta yadda za su tabbatar da samun moriyar siyasa mafi girma a cikin wannan takara.

Kafin a mika wannan shirin doka ga Mr. Bush, wato za a ware kudaden da yawansu ya fi wanda gwamnatin Bush ta nema, amma tilas ne a janye sojojin Amurka daga kasar Iraq kafin ran 1 ga watan Oktoba na wannan shekara, shugaba Harry Reid na jam'iyyun da suka sami rinjaye a majalisar dattijai ta Amurka da shugaba Nancy Pelosi ta majalisar wakilai ta Amurka 'yan jam'iyyar Dimokuradiyya sun sha bukatar Mr. Bush da ya sa hannu kan wannan shirin doka. Amma shugaba Bush ya yi barazanar yin watsi da ita a wurare daban daban.

Bayan da ya yi watsi da shirin dokar, a cikin jawabinsa a gidan talibijin, Mr. Bush ya nuna cewa, ko yaya ake ciki a Iraq, shirin dokar ta bukaci a soma janye sojojin Amurka daga Iraq kafin ran 1 ga watan Oktoba. Hakan zai sanya Iraq ta gamu da rashin kwanciyar hankali, zai kuma taimaki dakarun Iraq wajen tsara shirinsu bisa ajandar janye sojojin Amurka. Shirin dokar zai samar wa kwamandojin Amurka sharudda da yawa, ta haka ba za su iya daukar matakan soja ba sai bayan sun suka saurari shawara daga 'yan siyasa da ke birnin Washington.

A sa'i daya kuma, madam Pelosi ta bayyana cewa, shugaba Bush yana bukatar kudi da yawa amma ba tare da sharadi ba, majalisun dokoki na kasar ba za su ba shi ba. Ta kara da cewa, yana kasancewa da sabani mai tsanani a tsakanin majalisun dokokin da shugaba Bush, amma za su yi kokari don samun ra'ayi daya. Mr. Reid kuwa ya nuna cewa, ko da yake Mr. Bush ya yi watsi da shirin dokar, amma ba za su daina kokarinsu wajen neman canza manufofin Amurka dangane da yakin Iraq ba.

Saboda jam'iyyar Dimokuradiyya ba za ta iya samun isassun kuri'u a cikin majalisun dokokin kasar ba, shi ya sa zai yi wuya ta soke kudurin yin watsi da shirin dokar da Mr. Bush ya yi. A cikin irin wannan hali ne, ya zama wajibi ne majalisun dokokin kasar za su gabatar da sabuwar shirin doka, za su yi muhawara da kuma kada kuri'a a kanta, a karshe za su mika ta ga shugaba Bush don sa hannu a kai.

Masu nazarin harkokin yau da kullum suna ganin cewa, saboda bangarorin 2 wato majalisun dokokin kasar da shugaba Bush dukkansu ba su son daukar nauyin daidaita sakamakon da aka samu domin dakatar da biyan kudin soja ba, shi ya sa tabbas ne za su yi rangwame. Yanzu shugaba Bush na fuskantar babbar matsin lamba. Ya taba bayyana cewa, kudin soja ya yi kadan, idan majalisun dokokin kasar ba su zartas da shirin doka kan ware kudi domin yaki ba, to, babu sauran hanyar da za su zaba, sai sojojin Amurka su yi la'akari da rage kayayyakin soja da yi musu kwaskwarima da kuma raunana ingancin zaman rayuwarsu, ta haka za su iya yin tsimin wasu kudade don ci gaba da yaki. Sa'an nan kuma, sojan Amurka zai yi la'akari da rage horon da aka yi wa sojojinsa da ke Amurka. Idan ba a sami kudi a kwanaki 10 na tsakiya na watan Mayu ba, to, za a kawo illa ga horar da sabbin sojojin Amurka, ta haka za a kawo illa ga canzawa sojojin Amurka da aka girke a Iraq da Afghanistan.

Wasu kafofin yada labaru sun nuna cewa, a karshe dai majalisun dokokin kasar za su zartas da shirin doka da gwamnatin Amurka ke bukata kan ware kudi. Amma mai yiwuwa ne 'yan jam'iyyar Dimokuradiyya za su ware kudi kadan a ko wane karo don sanya muharawa kan batun Iraq za ta jawo hankulan jam'iyyun 2 wajen yin tattaunawar siyasa a tsakaninsu cikin dogon lokaci.(Tasallah)