Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-01 21:44:31    
Tsaunukan Cangshan

cri

Jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. Kamar yadda muka saba yi, da farko dai, za mu karanta muku wasu abubuwa kan tsaunukan Cangshan da ke lardin Yunnan, daga bisani kuma, sai wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Kallon zane-zanen jikin bango a gidan ibada na Pilusi'.(music)

Tsaunukan Cangshan na da nisan misalin kilomita 2 a tsakaninsu da birnin Dali na lardin Yunnan a yamma. A duk shekara kankara mai taushi na rufe kan babbar kololuwar tsaunukan mai suna Malongfeng, wadda tsayinta ya kai misalin mita 4122. Itatuwa kwarra da bishiyoyin shayi suna girma sosai a gangarar wannan babbar kololuwa. Ana iya samar da ganyayen shayi fiye da kilogram dubu dari 1 a ko wace shekara, wadanda aka gyara su a tsanake. Sa'an nan kuma, wurin ya yi suna ne a matsayin garin ganyayen shayi na farin ganyen shayi na Yunnan. Kazalika kuma, marmarar Dali wato Dali marble a Turance ta yi suna a duk kasar Sin a matsayin kayan gine-gine da na ado saboda tauri da launuka daban daban da kuma zane-zane masu ban sha'awa da ke kanta. An yi shekaru fiye da 1300 ana hakan shi a wannan yanki.

Idan masu yawon shakatawa sun je Dali a tsakanin watan Agusta da na Satumba, to, suna iya ganin gajimare mai ban sha'awa da ke tafiya a kewayen kololuwar Yujufeng ta tsaunukan Cangshan. An kira irin wannan gajimare 'Wangfuyun', wato wata mace na jiran mijinta. 'Yan kabilar Bai sun baza wannan almara game da wannan gajimare na Wangfuyun daga zuriya zuwa zuriya. An ce, yau da shekaru fiye da dubu daya da suka wuce, wato a zamanin daular Nanzhao, akwai wata kyakkyawar gimbiya mai suna A'feng, wadda 'yar sarkin daular Nanzhao ce, tana jin dadin zamanta a fada, wani mafarauci saurayi kuma jarumi wai shi A'long da ita sun shiga soyayya. Amma babbnta bai amince da ta auri A'long ba, shi ya sa suka gudu suka buya a kololuwar Yujufeng. Sarkin ya yi fushi sosai ya kama wannan mafarauci saurayi, ya kashe shi ya jefa gawarsa cikin tabkin Erhai. Daga baya gimbiya A'feng ita ma ta rasu saboda matukar bakin ciki da kuma fushi, ta zama farin gajirame. Tun daga nan ne a tsakanin watan Agusta da na Satumba na ko wace shekara, wannan gajimare ke bulla a kololuwar Yujufeng, ya yi kama da yadda gambiya A'feng take jiran mijinta A'long.

A tsaunukan Cangshan, gajimare da kankara mai taushi da kololuwa da kuma magangara su ne abubuwa 4 masu ban mamaki da ke jawon hankulan masu yawon shakatawa.

Tsaunukan Cangshan da kuma tabkin Erhai sun samar da kyawawan wurare masu ni'ima a Dali.