Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-01 18:19:13    
Sinawa suna nuna sha'awa sosai ga yin yawon shakatawa a lokacin dogon hutu

cri

Daga ran 1 zuwa ran 7 ga watan Mayu lokacin hutu ne mai tsawo na bikin "ran 1 ga watan Mayu" na kasar Sin, kuma yana daga daga cikin lokutan dogayen hutu 3 na kowace shekara. Sinawa wadanda sai kara yawa suke suna ta more lokutan hutu ta hanyar yin yawon shakatawa zuwa kasashen waje, amma har ila yau kasar Sin ta kama matsayi na farko na Asiya wajen kasuwar yawon shakatawa a kasashen ketare. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya rauwaito mana game da wannan labari.

Budurwa Shao Yun wata ma'aikaciya ce wadda take aiki cikin wani kamfanin birnin Beijing. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ta riga ta kashe kudinta na kanta don yin yawo shakatawa a kasashe da shiyyoyi da yawa a lokutan dogayen hutu. Ta ajiya hotuna da yawa da ta dauka da kayayyakin tunawa da ta saya a kan tebur din rubutu da shirgin littattfai na gidanta. Ta ce, tana shan aiki a zaman yau da kullum, a lokacin dogon hutu na "bikin ran 1 ga watan Mayu" na wannan shekara, ta yi shirin zuwa kasashen waje don yin yawon shakatawa cikin sakin jiki kuma tare da aminanta. Ta ce, "A da na kan je kasashen Asiya ta kudu maso gabas tare da aminaina, na taba zuwa bakin teku da cin abincin amfanin teku a kasar Singapore da ta Malasiya, na ji dadi sosai a wadannan wurare. A wannan gami kuwa a shirye nake zan yi yawon shakatawa a kasashen Turai. Na riga na yi rajistar shiga kungiyar yawon shakatawa domin cika wannan burina."

Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, mutane wadanda sai kara yawa suke sun yi kamar budurwa Shao sun yi yawon shakatawa a kasashen waje a lokutan hutu. Bisa kididdigar da aka yi an ce, yawan mutanen kasar Sin da suka yi yawon shakatawa a kasashen waje ya kai miliyan 34, wato ya karu da kashi 10 cikin 100 bisa na shekarar bariya.

A gabannin bikin "ran 1 ga watan Mayu", da akwai mutane da yawa wadanda suka je wajen manyan kamfanonin yawon shakatawa daban-daban na birnin Beijing don yin rajistar shiga kungiyoyin yawon shakatawa a kasashen waje a ko wace rana. Mr. Dun Jidong, mai kula da harkokin yawon shakatawa a kasashen waje na babban kamfanin yawon shakatawa na kasar Sin ya bayyana cewa, yawan mutanen da suka je kasashen waje domin yawon shakatawa a gun bikin "ran 1 ga watan Mayu" ya fi na zaman yau da kullum a kalla da kashi 30 bisa 100. Ya ce, "A galibi dai ana iya cewa, halin da ake ciki wajen yawon shakatawa a gun bikin "ran 1 ga watan Mayu" ya fi na shekarun baya kyau. Sinawa sun fi son zuwa kasashen Turai, ban da wannan kuma, da akwai Asiya ta kudu maso gabas ciki har da Tailand da Singapore da Malasiya da Indonesiya, kuma har da Japan da Korea ta kudu".

Yanzu yawan kasashe da shiyyoyi wadanda aka dauke su a matsayin wuraren da mutanen kasar Sin suka je yawon shakatawa sun riga sun kai fiye da 130. A gun wannan biki, dubu duban masu yawon shakatawa na kasar Sin za su je wurare masu ni'ima daban- daban na duniya, kuma sukan yi saye-saye da yawa, wannan zai kara samar da kudin shiga ga wadannan wurare. Madam Guo Lihua, shugabar ofishin yawon shakatawa ta kasar Austria da ke nan birnin Beijing ta ce, "Yawan mutanen kasar Sin da suka tafi kasar Austria domin kayawon shakatawa a shekarar 2006 ya kai dubu 176. Ban da wannan kuma, yawan kudaden da masu yawon shakatawa na kasar Sin suka ware domin sayen kayayyaki shi ma ya yi yawa., mun yi farin ciki a kan wannan."