A kwanan nan, ministan kiwon lafiya na kasar Sin Gao Qiang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta aika da likitoci masu yawa da ke aiki a cikin asibitocin birane zuwa kauyuka domin ba da ayyukan hidima, ta yadda za a iya kyautata halin da ake ciki wajen rashin daidaito tsakanin birane da kauyuka a fannin yin amfani da albarkatun jiyya, da kuma daga matsayin jiyya na yankunan kauyukan kasar Sin. Ban da wannan kuma ya jaddada cewa, za a tsara wani tsari domin gudanar da wannan aiki cikin dogon lokaci. To, yanzu ga cikakken bayani.
Ana iya samun albarkatun jiyya na kasar Sin da yawansu ya kai kashi 80 bisa dari a birane, amma kashi 20 bisa dari kawai ake iya samunsu a kauyuka. Domin kyautata halin rashin ci gaba da kauyukan kasar Sin ke ciki a fannin jiyya, kasar Sin tana cikin shirin zuba kudaden da yawansu ya kai Yuan biliyan 30 a cikin shekaru biyar masu zuwa domin raya kayayyakin kiwon lafiya na kauyuka. Ban da wannan kuma a cikin shekara ta 2005, hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta fara aikawa da likitoci fiye da dubu goma da ke aiki a birane zuwan kauyuka wajen tafiyar da ayyukan ba da hidima na jiyya da kuma horar da likitocin wurin.
Lokacin da ministan kiwon lafiya na kasar Sin Gao Qiang ya yi bayani kan batun, ya gaya mana cewa,
"Yanzu an riga an aika da masu aikin jiyya fiye da dubu goma na asibitoci manya da matsakaita 518 na biranen da ke tsakiya da kuma yammacin kasar Sin zuwa asibitoci da asibitocin likitancin gargajiya na kasar Sin da kuma cibiyoyin kiwon lafiya da yawansu ya zarce 1300 na wasu gundumomin kasar Sin. Kuma a cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata, sun riga sun yi jiyya ga mutane fiye da miliyan biyu, da kuma horar da masu aikin likitanci dubu 560 na wurin domin kyautata fasahar jiyya ta wurin."
An labarta cewa, yawancin asibitoci na kasar Sin suna karkashin jagorancin gwamnatin kasar, kuma likitoci su ne ma'aikata na gwamnatin kasar, shi ya sa gwamnatin tana iya aikawa da likitocin birane zuwa kauyuka wajen ba da ayyukan hidima na lokaci-lokaci. Kullum su kan yi aikinsu a kauyuka har shekara guda ko shekaru biyu. Bayan da suka fara aiki a kauyuka, likitocin birane su kan samar da sabbin fasahohin jiyya, musamman ma fasahohin da ke dace da halin da kauyuka ke ciki, ta haka an kyautata kwarewar aiki ta likitocin kauyuka. Ban da tafiyar da ayyukan ba da hidima da kuma shirya kwas din horaswa, asibitocin birane su kan ba da taimako ga asibitocin kauyuka wajen kyautata ayyukansu na gudanarwa da tsarin ka'idoji da kuma aikace-aikacen ba da hidima. Ta wadannan abubuwan da suka yi, ba kawai an kyautata kwarewar hukumomin jiyya na kauyukan kasar Sin wajen ba da hidima ba, har ma an rage nauyin da ke bisa wuyan manoma wajen ganin likita.
Game da wadannan likitocin birane da ke ba da taimako ga kauyuka, gwamnatin kasar Sin ta ba su gatanci a wasu fannoni. Alal misali, ana nuna musu fifiko a fannonin samun iznin daukaka da lambobin yabo da kuma damar shiga kwas din horaswa, ban da wannan kuma gwamnatin za ta samar da wasu kudade gare su. Mataimakin ministan kudi na kasar Sin Wang Jun ya bayyana cewa,
"a shekara ta 2005 da kuma shekara ta 2006, gwamnatin kasar Sin ta kebe kudaden da yawansu ya kai yuan miliyan 135 da kuma yuan miliyan 270 bi da bi wajen bai wa likitocin birane da suke aiki a kauyuka albashi da alawus da kuma kudin taimako. Ban da wannan kuma hukumomin kudi na wurare su ma sun kebe irin wadannan kudade. A nan gaba, hukumar kudi ta tsakiyar gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan tura likitoci dubu goma wajen ba da taimako ga kauyuka a fannin kiwon lafiya, da kuma ci gaba da kara yawan kudaden da za a zuba domin wurare mafiya yawa za su iya samun irin wannan taimako."
Bugu da kari kuma ministan kiwon lafiya na kasar Sin Gao Qiang ya bayyana cewa, a cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata, an samu sakamako mai kyau wajen aikawa da likitocin birane zuwa kauyuka domin ba su taimako, ta haka an sa kaimi ga cudanyar likitoci tsakanin birane da kauyuka, ta haka an sassauta rikicin da ke tsakanin birane da kauyukan kasar Sin wajen rashin samun bunkasuwar ayyukan jiyya cikin daidaici. Kuma ya kara da cewa,
"Aikin aika da likitoci dubu goma zuwa kauyuka wajen ba su taimako ya dace da halin da ayyukan kiwon lafiya na birane da kauyukan kasar Sin ke ciki, kuma dole ne a tsaya tsayin daka kan ci gaba da tafiyar da shi cikin dogon lokaci a nan gaba." (Kande Gao)
|