Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-30 14:28:32    
Takaitaccen bayani game da kabilar Tajik ta kasar Sin

cri

Yawancin 'yan kabilar Tajik suna zama a yankunan da ke kudu maso yammacin jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar ya kai dubu 41. Suna amfani da yarensu, kuma yawancinsu suna amfani da kalmomi da harufan Uygur.

Ko da yake yawan mutanen kabilar Tajik ya yi kadan, amma ta dade tana nan kasar Sin. Ma'anar Tajik a cikin yarensu ita ce "Kambin sarki".

Kafin kasar Sin ta shiga lokacin daular Qing, tattalin arziki da zaman al'umma na kabilar sun sami cigaba sannu a hankali. kasancewar babu kayan aiki na karfe a lokacin, suna yin amfani da kahon akuya domin saren gonaki. Amma bayan da aka shigar da kasar Sin a cikin lokacin daular Qing, a karkashin taimakawar kabilun Han da Uygur da Kirgiz, 'yan kabilar Tajik sun fara mallakar fasahohin noma da gina ayyukan ban ruwa da sarrafa kayayyakin dabbobi da hayayyafar da shannu da tumaki. Tattalin arziki da zaman al'ummar kabilar sun kuma fara samun cigaba.

A shekarar 1954, an kafa gundumar Tashkurken ta kabilar Tajik mai cin gashin kanta. Haka nan kuma, an fara kafa matsakaitun masana'antu ko kanana a yankunan kabilar ciki har da masana'antu masu aiki da karfin ruwa domin samar wa garuruwan kabilar Tajik wutar lantarki. A shekarar 1957, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta zuba jari ta shimfida wata hanyar mota da ke hade da birnin Kashi da garin Tashkurken. Ya zuwa yanzu, an riga an gina hukumomin gwamati da makarantu da asibiti da kantuna da bankuna da gidan waya da kulob a tudun Pamir. A da, yawan jahilai ya kai kashi 89 daga cikin kashi dari na duk yawan mutanen kabilar. Amma yanzu, kusan dukkan yara suna karatu a cikin makarantun firamare. An kuma gina wasu makarantun sakandare yayin da matasa da yawa na kabilar Tajik suke karatu kwalejoji da jami'o'in birnin Kashi da Urumqi har da a birnin Beijing.

A cikin dogon lokacin da ya wuce, 'yan kabilar Tajik sun kirkira wadatattun fasahohin zane-zane da adabi iri iri. 'Yan kabilar sun kware kan wakoki da raye-raye.

Bisa al'adar kabilar Tajik, wani saurayi yana iya auren mace daya. Zuriyoyin iyalai da yawa su kan zama tare.

Hular da 'yan kabilar suke sanya tana jawo hankulan mutane sosai. Maza su kan sanya hular baki. Amma mata suna sanya hular da aka saka furanni iri iri.

Galibin 'yan kabilar Tajik suna bin addinin Musulunci, amma babu masallaci a yankunan kabilar, kuma ba su yi azumin da aikin haji ba. Suna yin addu'a ne a lokacin bukukuwa kawai.

'Yan kabilar suna da bukukuwa iri iri ciki har da babbar sallah da karamar sallah.(Sanusi Chen)