Jiya 28 ga wata, a gun taron ministocin bangarori daban daban da ke shafe batun shiyyar Darfur da aka shirya a birnin Surt da ke gabashin kasar Libyan, shugaban kasar Mu'ammar al-Qadhafi ya la'anci dakarun da ke adawa da gwamnatin Sudan, sabo da suna da nufin mai da batun shiyyar Darfur da ya zama wani batun duniya.
Bisa labarin da muka samu an ce, a lokacin taron, Mr. Al-Qadhafi ya nuna cewa, bai kamata a yarda da ko wane bangaren da ba a amince da shi ba, ya sa baki a batun Darfur, sabo da wannan ya sabawa moriyar kasashen duniya.
Manzon musamman na babban sakataren M.D.D. da ke kula da batun Darfur Jan Eliasson ya bayyana cewa, matsalar shiyyar Darfur wata matsala ce mai tsanani sosai ga kasar Sudan, da duk shiyyar, har ma da duk duniya. Ya jaddada cewa, wannan taro shi ne wata damar da ke iya kara saurin warware matsalar Darfur, da aiwatar da yunkurin tabbatar da zaman lafiya. (Bilkisu)
|