Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-27 20:21:55    
An soma daukar masu aikin sa kai domin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008

cri

" Duniya daya kuma buri daya'. Wannan ya kasance kirarin ne na babban taken taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, wanda kuma yake nufin, cewa duk kowane mutumin duniya dake lura da taron wasannin Olympic zai iya samun damar shiga cikin yunkurin gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing. Ko da ka kasa shiga gasannin Olympic saboda wasu dalilai, amma har ila yau dai kana da damar shiga cikin yunkurin gudanar da wannan gagarumin taron wasannin a matsayin mai aikin sa kai. A ran 28 ga watan Maris na wannan shekara, a nan birnin Beijing, a hukumance ne aka soma daukar masu aikin sa kai domin taron wasannin Olympic na Beijing ga 'yan-uwa na yankin Hongkong da Macao da na Taiwan, da Sinawa 'yan kaka-gida dake zaune da kasashen ketare har da mutanen kasashen waje.

A maraicen ran 28 ga watan Maris na shekarar da muke ciki, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kira wani taron watsa labarai, inda ya sanar da soma daukar masu aikin sa kai, wato ke nan tun daga wannan rana ne 'yan-uwa na yankin Hongkong da Macao da na Taiwan, da Sinawa 'yan kaka-gida dake zaune a ketare da kuma mutanen kasashen waje su iya yin rajistan neman zama masu aikin sa kai domin taron wasannin Olympic na Beijing. Mr. Li Binghua, mataimakin shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing kuma mataimakin shugaban kungiyar sulhuntawa ta masu aikin sa kai ta taron wasannin Olympic na Beijing ya furta, cewa an rigaya an soma daukar masu aikin sa kai daga dukkan fannoni domin taron wasannin Olympic da kuma na nakasassu. Muna lale marhabin da mutane daga da'irori daban-daban wadanda suka dace da muhimman sharuda da su yi rajistan neman zama masu aikin sa kai domin yin aikin hidima da kyau ga wadannan tarurrukan wasannin Olympic guda biyu.

Sa'annan Mr. Li Binghua ya bayyana, cewa kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing da kuma kungiyar sulhuntawa ta masu aikin sa kai ta taron wasannin Olympic na Beijing za su danka nauyi ga hukumomin da abun ya shafa don gudanar da harkokin daukar masu aikin sa kai. A watan Mayu na shekara mai zuwa ne, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing zai kammala wannan aiki, kuma zai aike da takardun sanarwa kan karbar masu aikin sa kai cikin lokaci.

Jama'a masu sauraro, bisa labarin da muka samu, an ce, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing yana bukatar dimbin masu aikin sa kai wadanda suke jin harsunan waje. Yanzu, ana karancin masu aikin sa kai dake iya yin magana da wasu harsunan waje. Don haka ne dai, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing yana fatan mutanen da'irori daban-daban na gida da na waje wadanda suke jin harsunan waje za su nuna himma wajen yin rajista. Daga baya, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing zai zabi wasu mutane wadanda suke iya yin magana da harshen Sinanci da kuma harsunan waje musamman ma wasu kananan harsunan waje da ake karancinsu don su shiga cikin rukunin masu aikin sa kai.

Mr. Liu Jian, shugaban ofishin kungiyar sulhuntawa ta masu aikin sa kai na taron wasannin Olympic na Beijing ya bayyana, cewa akwai masu aikin sa kai da yawansu ya kai dubu dari daya da za su yi aikin hidima ga taron wasannin Olympic da kuma na nakasassu na Beijing. Akasarin masu aikin sa kai da za a dauka, dalibai ne na jami'o'I da kolejoji na Beijing. Kuma za a dauki wasu mutane masu aikin sa kai daga mazaunan larduna da birane da kuma na jihohi masu cin gashin kansu na cikin babban yankin kasar Sin, da 'yan-uwa na Hongkong da Macao da kuma na Taiwan, da Sinawa 'yan kaka-gida dake zaune a ketare da kuma wasu mutanen kasashen waje.

A karshe dai, Mr. Liu Jian ya fadi, cewa kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing zai bada tabbacin ayyuka ga masu aikin sa kai na taron wasannin Olympic na Beijing, ciki har da samar da katin rajistan shaidar asalinsu, da tufafin aiki, da abinci da kuma kudin inshora na matsalolin ba-zata da dai sauransu. Mutane masu aikin sa kai wato 'yan-uwa na Hongkong da Macao da na Taiwan, da Sinawa 'yan kaka-gida dake zaune a kasashen waje da kuma mutanen kasashen ketare su ma za su iya samun wannan tabbaci da kuma takardun shaidawa da lambobi har da kyaututtuka na taron wasannin Olympic da na nakasassu na Beijing daga kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing.

Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya taba fadin,cewa shekarar 2008, murmushi na masu aikin sa kai ya kasance tamkar wani kati ne mafi kyau na Beijing. ( Sani Wang )