Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-27 20:16:39    
Ana kokarin farfado da shahararrun tsoffafin kantuna a birnin Wuxi na kasar Sin

cri

Birnin mai suna Wuxi wani shahararren tsohon birne ne a kudu maso gabashin kasar Sin, kuma yana daya daga cikin wurare da suka fara bunkasa masana'antu da kasuwanci a kasar Sin tun can da. Haka kuma ya kasance da tsoffafin kantuna da yawa a birnin wadanda suka shahara sosai a gida da waje. A cikin shekarun nan da suka wuce, bisa taimakon da hukumar birnin ta bayar da kuma kokari da irin wadannan kantuna ke yi, an farfado da kantunan nan sosai.

Da jama'ar Sin suka tabo magana a kan birnin Wuxi, ko shakka babu, za su tuna da manyan kayayyakin musamman 3 da ake samu a birnin, kamar kayayyakin tangaran na wasan yara, da wani irin abincin gargajiya da ake yi da wake da aka soya cikin man girki, da kuma nama da aka dafa cikin romon soya. Wani kanti mai suna "Sanfengqiao" yana sayar da irin wannan nama da ya shahara sosai a binrin da sauran wuraren kasar Sin da na waje.

Ba ma kawai mazaunan birnin Wuxi suna sha'awar namar ba, har ma mutane na sauran wurare ma suna sha'awarta ainun. Malam Xu Qing wanda ya fito daga birnin Shanghai ya gaya wa wakilinmu cewa, ya zo birnin Wuxi daga birnin Shanghai mai nisan sama da kilomita 100 musamman domin sayen naman. Ya ce, "na zo birnin ne daga birnin Shanghai musamman domin sayen irin wannan nama daga kantin "Sanfengqiao". Tun can da, na san wannan tsohon kanti, a duk lokacin da na zo birnin, ko shakka babu, na sayi namar mai dadin ci kwarai."

Bisa kokarin da aka yi a cikin shekaru da yawa da suka wuce, yanzu, kanti ya riga ya sami ci gaba har ya zama wani babban kamfani, wanda ke da kananan kantuna 13, nauyin irin wannan nama da yake dafawa ya kan wuce tan 5,000 a ko wace shekara, yawan kudin shiga da yake samu daga wajen sayar da naman ya kai kudin Sin Yuan miliyan 100. Yanzu, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta riga ta mayar da kantin nan don ya zama daya daga cikin shahararrun tsoffafin kantunan kasar.

Malam Hu Yaomin, shugaban kwamitin gudanarwa na kamfanin "Sanfengqiao" ya bayyana cewa, "wajibi ne, shahararren tsohon kanti ya bunkasa harkokinsa ta hanyar kirkire-kirkire. Idan abubuwa da kantin ke sayarwa ba su dace da bukatun jama'a ba, to, zai sha hasara. Sabo da haka wajibi ne, mu yi kirkire-kirkire a fannin ingancin kayayyakin da ire-irensu da kuma hanyyar da ake bi wajen gudanar da harkokin kantin. "

A birnin Wuxi, ban da kantin "Sanfengqiao", kuma akwai shaharrun tsoffin kantuna da yawa wadanda ke gunadar dakunan cin abinci da kantunan sayar da kayayyakin masarufi da na abinci da magungunan sha da sauransu.

Malam Huang Jianhua, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya ta birnin Wuxi yana ganin cewa, shahararrun tsoffafin kantuna tsoffafin kayayyakin al'adu ne masu daraja sosai. Yanzu, birnin ya fara daukar matakai daban daban don farfado da su. Ya bayyana cewa, "shahararrun tsoffafin kantuna suna nuna wani irin al'adun gargajiya na birninmu, kuma ya wakilci ci gaba da aka samu wajen bunkasa aikin masana'antu da harkokin kasuwanci a birnin, dukanninsu suna da ikonsu na mallakar ilmi da ba safai a kan iya samunsu ba a sauran wurare. A farkon shekarar nan, mun fara tsara shirin farfado da su. Idan mun gudanar da ayyukanmu da abin ya shafa da kyau, to, shahararrun tsoffafin kantuna na birnin Wuxi za su kara taka muhimmiyar rawarsu sosai."

Malam Huang Jianhua ya kara da cewa, don farfado da shahararrun tsoffafin kantuna na birnin Wuxi, hukumar birnin za ta tallafa su ta hanyar sa kaimi ga gyare-gyaren tsarin kantuna da ba da rancen kudi da kiyaye tsoffafin kayayyakin al'adu da ikon mallakar ilmi da sauransu. (Halilu)