 A ran 26 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, ana bukatar yin namijin kokari a fannin diplomasiyya wajen warware batun shiyyar Darfur ta kasar Sudan a maimakon sanya takunkumi.
Lokacin da Ban Ki-moon ke zantawa da manema labarai a babban zauren MDD, ya bayyana cewa, har kullum batun Darfu wani batu ne da ke jawo hankulan MDD da kasashen duniya, muddin an yi namijin kokari a fannin diplomasiyya, to za a iya samun sakamako mai kyau a cikin shawarwarin da ya samu ci gaba kadan.
Ban da wannan kuma Mr. Ban ya jaddada cewa, yanzu MDD ta riga ta fara yin aiki na mataki na biyu na jibge sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da kungiyar tarayyar Afirka a shiyyar Darfur. Kuma yana iyakacin kokari wajen lallashin gwamnatin Sudan wajen amincewar aiki na mataki na uku, wato jibge sojojin kiyaye zaman lafiya dubu 20 a Darfur.(Kande Gao)
|