Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-26 22:22:16    
An sanar da wutar Yola ta wasannin Olympics na Beijing da kuma hanyar da aka tsara wajen mika ta

cri

Yau 26 ga wata da dare a nan birnin Beijing, kwamitin kula da wasannin Olympics na Beijing ya sanar da wutar yola ta wasannin Olympics na Beiijing da kuma hanyar da aka tsara wajen mika ta.

Wutar Yola ta wasannin Olympics na Beijing tana da tsawon centimita 72, kuma nauyinta ya kai gram 985, kuma an tsara ta ne bisa ra'ayin "asali daya da zaman jituwa".

Bayan haka, kwamitin kula da wasannin Olympics na Beijing ya kuma sanar da hanyar da aka tsara wajen mika wutar yola ta wasannin Olympics. Babban jigon aikin nan na mika wutar yola shi ne "hanya mai jituwa". Wutar Yolar za ta tashi daga birnin Beijing daga ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2008 mai zuwa, kuma za ta yada zango a birane 22 da ke kasashen ketare da kuma birane da yankuna 113 da ke nan kasar Sin, kuma za ta dawo babban filin wasannin Olympics da ke birnin Beijing a lokacin da ake bude wasannin Olympics a ran 8 ga watan Agusta na shekarar 2008 da dare. An ce, za a shafe kwanaki 130 ana mika wutar yolar, kuma tsawon hanyar ya kai har kilomita dubu 137.(Lubabatu)