Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-26 20:02:42    
Saukakakken tarihi na Zeng Qinghong

cri

Jama'a masu sauraro,muna fatan za ku cigaba da sauraron shirye-shiryenmu.Ga shi yanzu muna gabatar da Mr Zeng Qinghong wanda shi ne manban dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,sakataren sashen sakatariya na tsakiya kuma mataimakin shugaba na Jamhuriyar Jama'ar Sin.

Mr Zeng Qinghong,an haife shi a watan Yuli na shekara ta 1939 a wurin Ji An na lardin Jiangxi,ya shiga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a watan Afril na shekara ta 1960,a watan Yuli na shekara ta 1963 ne ya fara aiki bayan da ya kammala karatunsa a sashen koyon ilimin automatic control na Jami'ar masana'antu ta birnin Beijing shi kuma injiniya ne.Daga shekara ta 1958 zuwa shekara ta 1963 ya yi karatu a sashen koyon ilimin automatic control na Jami'ar masana'antu ta birnin Beijing.Daga shekara ta 1963 zuwa shekara ta 1965 ya kasance mallamin fasaha na rukunin 743 na rundunar soja ta yantar da jama'a ta kasar Sin.Daga shekara ta 1965 zuwa shekara ta 1969,shi mallamin fasaha ne a ofishi na shida na sashe na biyu ta cibiya ta biyu a ma'aikatar injuna ta bakwai ta kasar Sin.Daga shekara ta 1969 zuwa shekara ta 1970 ya yi aiki a sansanin Chikan na rukunin soja na Guangzhou da sansanin aiki na tafkin yamma na lardin Hunan.Daga shekara ta 1970 zuwa shekara ta 1973 ya kasance mallamin fasaha a sashe na biyu na cibiya ta biyu ta ma'aikatar injuna ta bakwai.Daga shekara ta 1973 zuwa shekara ta 1979,shi mallamin fasaha ne a sashen kula da masana'antu na ma'aikatar tsaron kasa na birnin Beijing da sashen kula da harkokin kimiyya da fasahohin.Daga shekara ta 1979 zuwa shekara ta 1981,shi sakatare ne a ofishin kwamitin tsare tsare na gwamnati.Daga shekara ta 1981 zuwa shekara ta 1982,shi mataimakin shugaba na ofishin kwamitin kula da makamashi na gwamnati.Daga shekara ta 1982 zuwa shekara ta 1983 ya yi aiki a sashen cudanya na hukumar kula da harkokin waje na ma'aikatar man fetur.Daga shekara ta 1983 zuwa shekara ta 1984,ya kasance mataimakin manaja na sashen cudanya na babban kamfanin man fetur daga tekuna na kasar Sin,mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin waje na ma'aikatar man fetur da kuma sakatare na kwamitin jam'iyyar na kamfanin man fetur da ke kudancin rawayen teku.Daga shekara ta 1984 zuwa shekara ta 1986,ya kasance mataimakin shugaba da shugaba na sashen tsare tsare na kwamitin birnin Shanghai kuma zaunannen manban kwamitin birnin da sakatare-janar na kwamitin.Daga shekara ta 1986 zuwa shekara ta 1989,shi mataimakin sakatare ne na kwamitin birnin Shanghai.Daga shekara ta 1989 zuwa shekara ta 1993,shi mataimakin darektan ofishin gwamnatin tsakiya.Daga shekara ta 1993 zuwa shekara ta 1997,shi ne darektan ofishin gwamnatin tsakiya kuma sakatare na kwamitin kula da harkokin ma'aikatun da ke karkashin gwamnatin tsakiya.Daga shekara ta 1997 zuwa shekara ta 1999,ya kasance manba da na ba cikakke ba na ofishin siyasa na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,da sakataren sashen sakatariya na tsakiya,kuma darektan ofishin tsakiya,da sakatare na kwamitin kula da harkokin ma'aikatu dake karkashin tsakiya kai tsaye.Daga shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2002,ya kasance mamba da na ba cikakke ba na ofishin siyasa na tsakiya da sakataren sashen sakatariya na tsakiya da shugaban ma'aikatar kula da tsare tsare na tsaakiya.Daga shekara ta 2002 ya zama mamban dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma sakataren sashen sakatariya na tsakaiya da shugaban makarantar jam'iyya ta tsakiya.(daga watan Disamba na shekara ta 2002 ya kuma samu wannan kujera),a taro na farko na kwamiti na 10 daaka yi a watan Maris na shekara ta 2003 aka zabe shi da ya zama mataimakin shugaban Jamhuriyar Jama'ar Sin.

Mr Zeng Qinghong ya kasance manban kwamitin tsakiya na 15 kuma mamba da na ba cikakke ba na ofishin siyasa na tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da sakataren sashen sakatariya na tsakiya.ya kuma kasance mamban kwamitin tsakiya na 16 da mamban ofishin siyasa na tsakiya,da manban dindindin na ofishin siyasa da sakataren sashen sakatariya na tsakiya.

Jama'a masu sauraro,kun dai saurari saukakakken tarihi na mataimakin shugaban Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin Mr Zeng Qinghong.