Ran 26 ga wata ranar kare ikon mallakar ilmi ta bakwai. A wannan rana, Mr. Jiang Zengwei, direktan ofishin rukunin aiki na kare ikon mallakar ilmi na kasar Sin ya bayar da wani jawabi a gidan rediyonmu, wato CRI, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana da karfi da niyyar kare ikon mallakar ilmi. A waje daya, kasar Sin za ta ci gaba da kara yin aikin kare ikon mallakar ilmi da yin yaki da laifuffukan satar ikon mallakar ilmi tare da karfafa aikin kare ikon mallakar ilmi ta hanyar shari'a domin bincike kan laifuffukan satar ikon mallakar ilmi bisa doka. Mr. Jiang ya ce, "Gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayin kare ikon mallakar ilmi. Sakamakon da ta samu wajen kare ikon mallakar ilmi yana jawo hankulan mutane sosai. Ba ma kawai tana tsara wani cikakken dokokin kare ikon mallakar ilmi ba, hatta ma tana tsara wani cikakken tsarin aiwatar da wadannan dokoki domin kare ikon mallakar ilmi bisa doka. Bugu da kari kuma, tana kokarin kafa wani kyakkyawan muhalli na kare ikon mallakar ilmi a duk zaman al'ummarta."
Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen kare ikon mallakar ilmi a kullum. Musamman bayan shigarta cikin kungiyar cinikayya ta duniya, wato WTO, kasar Sin ta riga ta kafa ka'idoji da dokokin da suke dacewa da ka'idojin da dokokin da yawancin kasashen duniya suke bi domin kare ikon mallakar ilmi. A waje daya, ta gano wasu manya da muhimman matsalolin satar ikon mallakar ilmi.
Bisa kididdigar da aka yi, an kwashe kayayyakin jabu fiye da miliyan 73 da aka saci ikon mallakar fasaharsu a shekarar bara kawai. Haka kuma, kasar Sin ta kafa cibiyoyin karbar sukan da ake yi kan laifuffukan satar ikon mallakar ilmi a manya ko matsakaitan birane 50. Amma a waje daya, Mr. Jiang Zengwei ya nuna cewa, har yanzu ya kasance da wasu matsaloli a kasar Sin wajen kare ikon mallakar ilmi. Mr. Jiang ya ce, "Har yanzu, tsarin aiwatar da dokokin kare ikon mallakar ilmi a kasar Sin yana aiki amma ba kamar yadda muke fata ba. Ba za a iya aiwatar da manufofin da suke dacewa da dokokin kare ikon mallakar ilmi kamar yadda ake fata ba. Wasu masana'antu wadanda suke neman bunkasuwa a kasuwanni ba su iya kare ikonsu na mallakar ilmi bisa doka ba lokacin da suke nazari da kere-kere tare da kuma sayar da kayayyakinsu. A waje daya kuma, ba su da isashen ilmi da karfin kare ikonsu lokacin da suke samun rikice-rikice kan batun kare ikon mallakar ilmi."
Duk da haka, kasar Sin tana da niyyar kyautata aikinta wajen kare ikon mallakar ilmi, a cewar Jiang Zengwei. An bayar da labari cewa, a shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta kara karfin kare ikon mallakar ilmi tare da kuma kara karfin yaki da laifuffukan satar ikon mallakar ilmi. Musamman za ta kara mai da hankali kan yadda za a kare ikon mallakar ilmi bisa doka. Kuma za a yi shari'a kan laifuffukan satar ikon mallakar ilmi bisa doka. Sabo da haka, Mr. Jiang Zengwei ya ce, "A shekarar 2007, kasar Sin za ta kara karfin yin shari'a kan laifuffukan satar ikon mallakar ilmi domin yanke hukunci kan manyan laifuffukan da suke da nasaba da satar ikon mallakar ilmi bisa doka. A waje daya, za ta kara mai da hankali wajen daidaita wasu kananan laifuffukan da suke kuma da nasaba da ikon mallakar ilmi. Bugu da kari, za ta kara kyautata odar yin takara a kasuwanni da kare sabbin kirkire-kirkiren da aka samu. Haka kuma, za ta kara mai da hankali wajen kiyaye moriyar halal ta mutane ko kamfanoni na gida da na waje cikin halin zaman daidai wa daida domin ciyar da kasuwar sabbin sana'o'i gaba lami lafiya."
Kazalika, Mr. Jiang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kyautata tsarin kare ikon mallakar ilmi da kyautata muhallin kirkire-kirkire tare da kuma kara kyautata tsarin daidaituwa a tsakanin yankuna daban-daban domin kare ikon mallakar ilmi. Mr. Jiang ya ce, "Kasar Sin za ta sauke nauyin kare ikon mallakar ilmi da ke bisa wuyanta kamar yadda ya kamata. Wannan kuma wani wajababben zabi ne da kasar Sin ta yi lokacin da ake raya ta da ta zama wata kasar da take da karfin kirkirar sabbin fasahohi tare da kuma lokacin da ake raya tattalin arzikin duniya bai daya. Sabo da haka, ko shakka babu dole ne kasar Sin ta kara karfin kare ikon mallakar ilmi." (Sanusi Chen)
|