Bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin suna da tarihin da yawan shekarunsu ya kai dubu biyu ko fiye, su ne abubuwan tarihi na al'adu da jama'ar kasar Sin suka samu bayan da suka dudduba da nazari da kuma takaita abubuwa kan yanayin sararin samaniya cikin 'yanci kuma cikin dogon lokaci. Suna iya bayyana sauye-sauyen yanayin sararin samaniya da ruwan sama da sauran sauye-sauyen da aka samu bisa yanayin sararin samaniya da kuma ba da jagoranci ga ayyukan noma, sun ba da tasiri sosai ga abinci da sutura da tafiye-tafiye na duban iyalai. A takaice dai, an kasa shekara daya cikin matakan lokaci 24 bisa yanayin sararin samaniya, a kowane matakin, alamar yanayin sararin samaniya ta zauna cikin zaman karko, kuma an dora matakin da wani suna. Bikin Qingming ya kan zo a ranar 4 ko biyar ko shida na watan Afril. Bikin Qingming na shekarar da muke ciki zai zo ne a ranar 5 ga watan Afril .
Game da asalin samun sunan Qingming, an bayyana a cikin tsofaffin littattafai na zamani aru-aru cewa, dukkan tsire-tsiren halittu suna tsiro da girma, kuma an sami tsabta da haske sosai a lokacin bikin Qingming , shi ya sa ana cewa, ya kasance da tsabta da haske ke nan a ranar bikin qingming. In ranar bikin Qingming ta zo, sai ake kara ruwan sama da yawa , lokacin ya yi daidai lokaci mai kyau na yin shuke-shuke da sauran aikin noma, saboda haka, akwai karin magana na manoma cewa, kafin ranar bikin Qingming da bayanta, ana soma shuke-shuken wake da ganyayen lambuna da dai sauransu tare kuma dasa bishiyoyi, kada a bata lokacin bikin Qingming. Kai, a gaskiya dai bikin yana da danganta da aikin noma sosai da sosai.
Qingming biki ne na halittu, sa'anan kuma shi ne bikin al'adun gargajiya na kasar Sin mai muhimmanci da al'ummar kasar Sin suke yi bikin tunawa da kakani-kakaninsu, yanzu, an riga an mayar da bikin don ya shiga cikin littafin rubuta sunayen abubuwan tarihi na duniya ba na kayayyaki ba . sakamakon da aka samu bayan bincike, an bayyana cewa, bikin Qingming yana da tarihin da yawan shekarunsa ya wuce 2500. An tsai da cewa, ranar somawar yanayin sararin samaniya ta Qingming ita ce ranar bikin Qingming, amma mutane suna saba da cewa, ranar 5 ga watan Afril ita ce ranar bikin Qingming.
Nuna bikin tunawa da mutanen iyalan da suka riga-mu gidan gaskiya a gaban kabaransu aiki ne mai muhimmanci da aka yi a ranar bikin Qingming. Kabilar Han da sauran kananan kabilu su ma suna da al'adar. A hakika dai ne, a cikin kauyukan kasar Sin, a ranar bikin Qingming, mutane suna tafiya zuwa huruman kakani-kakaninsu da na danginsu tare da giya da abinci da 'ya'yan itatuwa da kyandir da turare da sauransu, sa'anan kuma sun kone kyandir da turare, sun ajiye abinci a gaban kabaran danginsu, kuma sun kara sanya sabbin kasa a kan kabaran tare da yanke wasu rassan bishiyoyi don dasa su a kan kaburan, kuma suna yin sujada tare da watsa giya da abinci a gaban kaburan . Wasu ajiyayyun takardu sun bayyana cewa, a ranar bikin Qingming , ana ruwan sama a wurare da yawa a kasar Sin, wannan ya kara sanya mutane cikin tunanin danginsu da suka riga mu gidan gaskiya, wani mashahurin mawaki na karni na 9 mai suna Du Mu ya taba rubuta halin nan na musamman da ake ciki da cewa, ana ta ruwan sama , mutanen da ke tafiya a kan hanya suna cikin bakin ciki sosai tamkar yadda za su mutu bisa sakamakon tunawa da danginsu da suka riga mu gidan gaskiya.
Ya zuwa yanzu, mutanen kasar Sin suna ci gaba da bin al'adar nan ta tunawa da kakani-kakaninsu a ranar bikin Qingming. Yanzu saboda ko a birane ko a kauyuka, ana kan kona gawawakin matattu, shi ya sa mutane su kan tafi zuwa huruman jama'a a ranar bikin Qingming don ajiye furanni a gaban kaburan danginsu .
Amma ba bikin tunawa da kakani-kakanin mutane da aka yi a ranar bikin Qingming kawai ba, ana kuma mayar da ranar bikin don ta zama ranar yawon shakatawa duk saboda yanayin sararin samaniya ya soma zafi, kuma bishiyoyi da ciyayi sun soma tsiro da sabbin ganyayye, shi ya sa ranar ta zama lokaci mai kyau da ake yin yawon shakatawa.(Halima)
|