Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-25 21:04:06    
Oriented Pearl TV tower dake birnin Shanghai

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Sanusi Isah Dankaba, mazaunin birnin Keffi da ke jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya. Malam Sanusi Isah Dankaba, mai sauraronmu ne a kullum, kuma ya sha aiko mana tambayoyinsa. A cikin wata wasikar da ya turo mana a kwanan baya, ya tambaye mu, Oriented Pearl TV tower dake tsaye gab da bakin teku a birnin Shanghai, wanda shi ne cibiyar kasuwanci ta kasar Sin, wannan hasumiya mai tsawon gaske, shin ta kai mita nawa kuma ko tana daya daga cikin gini mafi tsawo a duniya?

Birnin Shanghai wani muhimmin birni ne da ke gabashin kasar Sin, wanda ke da dadadden tarihi da kuma al'adun gargajiya. A birnin Shanghai, ana iya samun muhimman wuraren tarihi masu yawa. Amma Shanghai shi kuma wani birni ne na zamani, wanda har ya kasance cibiyar kasuwanci da ta kudi ta kasar Sin da kuma wata muhimmiyar tashar jiragen ruwa ta duniya da ke shiyyar yammacin tekun Pasifik. Tun daga shekarun 1990, Shanghai ya gina jerin gine-gine na zamani, wadanda suka nuna wa duniya sabuwar fuskar Shanghai, kuma oriented Pearl TV tower, wato hasumiyar telebijin ta Shanghai tana daya daga cikinsu.

Hasumiyar telebijin ta Shanghai tana gabar kogin Huangpu, kuma tsawonta ya kai mita 468, sabo da haka, ta zamanto hasumiya mafi tsayi a nahiyar Asiya da kuma ta uku a duk duniya baki daya, wato bayan hasumiyar TV da ke birnin Toronto na kasar Canada da kuma birnin Moscow na kasar Rasha.

Abin da wannan hasumiya ta fi sha bamban da sauran hasumiyoyi shi ne, a jikinta akwai wasu kwallaye 11 iri daban daban wadanda suka barbaje daga sama har zuwa kasa, kuma sun kasance tamkar wasu jerin lu'u lu'u ne. Hasumiyar tana kunshe da manyan ginshikai uku wadanda ke da fadin da'ira na mita 9, da dakin 'yan sama jannati da wani kwallon da ke sama da wani daban da ke kasa da wasu kananan kwallaye biyar da gindin hasumiyar da kuma wani fili. A cikin kwallon da ke sama, akwai wani hawan da ke da tsayin mita 263 daga sararin kasa inda ake iya kalle-kalle?shi wuri ne mafi kyau a wajen kallon birnin Shanghai daga sama. A cikin kwallon kuma, akwai wani hawa daban da ke da tsayin mita 267 daga kasa, inda akwai wani dakin cin abinci da ke iya juyawa da kuma wani dakin rawa da dakin rera wakoki wadanda bude suke ga masu yawon shakatawa.

An dai gina dakin 'yan sama jannati a wurin da ke da matukar tsayi, wanda har ya kai mita 350 daga sararin kasa. A cikin dakin, akwai wurin kallo da dakin taro da kuma zauren shan kofi. Sa'an nan, a cikin kananan kwallaye biyar, an kuma gina masaukan baki har 20. A cikin hasumiyar kuma, akwai wani babban kantin da fadinsa ya kai muraba'in mita dubu 18, inda ake sayar da tufafi da kayayyakin sassaka na hannu da abubuwan ado da abinci da sauransu, ta yadda masu yawon shakatawa za su iya jin dadin sayayya da kuma abinci a yayin da suke yawon shakatawa.

A karkashin hasumiyar kuma, akwai wani birnin ilmin hasashen kimiyya, inda masu yawon shakatawa ke iya kama hanyar zuwa duniya mai cike da abubuwan kasada da kuma kallon fina-finai na zamani.

Bayan haka, a cikin hasumiyar, akwai wani gidan nune-nunen kayayyakin tarihi na Shanghai, inda ake nuna kayayyakin tarihi da takardu da hotuna da fina-finai wadanda suka bayyana bunkasuwar birnin Shanghai da kuma sauye-sauyen da ya samu a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma da dai sauransu a cikin shekaru kusan dari da suka wuce.

Kasancewarta wuri na yawon shakatawa da tarurruka da cin abinci da sayayya da nishadi da kuma wurin kwana da kuma wuri na hasumiyar ba da sigina na telebijin, hasumiyar TV ta Shanghai ta riga ta zama wata alama ta birnin Shanghai. A halin yanzu dai, yawan masu yawon shakatawa da ke zuwa hasumiyar a kowace shekara ya zo na biyu daga cikin dukan hasumiyoyi masu tsayi na duniya, wato bayan hasumiyar Eiffel da ke kasar Faransa. Sakamakon haka kuma, ta zamanto daya daga cikin shahararrun wuraren shakatawa na duniya.

Malam Sanusi Isah da dai sauran masu sauraronmu, idan kun sami damar zuwa birnin Shanghai, kada dai ku wuce hasumiyar TV ta birnin.(Lubabatu)