Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-25 08:26:07    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (18/04-24/04)

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya bayyana cewa,an riga an kammala shirin zaben hanyar gudun yada kanin wani na mika wutar yola ta wasannin Olimpic na Beijing lami lafiya,kuma an riga an gama aikin shirya wutar yola ta wasannin.A ran 26 ga wata,a hukunce ne za a sanar da wannan shiri a dandalin karni na kasar Sin dake nan birnin Beijing.

Ran 23 ga wata,shugaban kwamitin wasannin Olimpic na duniya Mr.Jacques Rogger ya sauka nan birnin Beijing kuma ya fara ziyara ta kwanaki biyar a birnin.Mun sami labari cewa,Mr.Rogger ya zo Beijing ne don halartar babban taron wasannin motsa jiki na duniya da aka saba yi sau daya a kowace shekara,ban da wannan kuma,zai shugabannci taron kwamitin zartaswa na kwamitin wasannin Olimpic na duniya,a gun wannan taro,za a karanta rahotanni game da aikin shirya taron wasannin Olimpic na shekarar 2008 na Beijing da taron wasannin Olimpic na shekarar 2012 da za a yi a birnin London na kasar Ingila da sauransu.Za a yi babban taron wasannin motsa jiki na duniya daga ran 24 zuwa ran 27 ga wannan wata a birnin Beijing na kasar Sin.Wakilai daga hadaddun kungiyoyyin wasannin motsa jiki na duniya da kwamitin wasannin Olimpic na duniya da sauran fannoni daban daban dake da nasaba da wasannin motsa jiki fiye da dubu daya za su halarci taron.Wannan taro shi ne taro mafi girma da kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya shirya a tarihinsa.

Ran 21 ga wata ne,aka fara gasar cin kofin Asiya ta wasan daukan nauyi ta shekarar 2007 a birnin Tai`an na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin.a gun gasa ta ajin kilo 48 ta mata,`yar wasa daga kasar Sin Chen Xiexia ta kago wani sabon matsayin bajimtar duniya na kilo 120 na daukan nauyi na sabawa.Wannan ne karo na farko da Chen Xiexia ta shiga irin wannan babbar gasa ta nahiya.(Jamila zhou)