Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-25 08:23:02    
Wasan kwallon golf ya sami ci gaba a kasar Sin

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba,a birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin,aka yi budaddiyar gasar wasan kwallon golf ta VOLVO ta shekarar 2007 wato `VOLVO golf China open`.A gun gasannin da aka shirya a cikin kwanaki hudu da suka shige,`dan wasa daga kasar Austria Marcus Brier ya zama zakara.Ban da wannan kuma,abu mafi jawo hankulan mutanen kasashen duniya shi ne,a cikin `yan wasa 75 wadanda suka shiga zagaye na karshe na gasar domin daga matsayi,yawan `yan wasa daga kasar Sin sun kai 7,wannan karo na farko ne da kungiyar kasar Sin ta samu irin wannan sakamako mai faranta ran mutane a tarihin gasar yawon kasa kasa ta Turai.`Yan wasan kwallon golf samari da suka zo daga babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan na kasar Sin sun yi kokari kuma sun samu ci gaba a kai a kai,ko shakka babu,wannan zai ciyar da wasan kwallon golf gaba a kasar Sin.

Kungiyar wasan kwallon golf ta kasar Sin ta shirya budaddiyar gasar wasan kwallon golf ta kasar Sin ta VOLVO,a kan shirya gasar yawon kasa kasa a Turai da Asiya,zuwa yanzu,tarihinta ya riga ya kai shekaru 13.A gun wannan gasar da aka shirya,`yan wasa daga babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan na kasar Sin 7 sun shiga zagaye na karshe na gasar,ba a taba samun irin wannan hali ba a da.Wadanda a cikinsu,Ye Jianfeng daga babban yankin kasar Sin ya kai shekaru 15 da haihuwa ne kawai,Han Ren daga babban yankin kasar Sin shi ma ya kai shekaru 17 da haihuwa ne kawai,ban da wannan kuma,Pan Zhengzong da Pan Fuqiang daga Taiwan na kasar Sin sun kai shekaru 15 da 19 da haihuwa,wadannan `yan wasa biyu sun zo ne daga iyali daya wato su `yan uwa ne.Abun mamaki shi ne a halin da ake ciki yanzu,wadannan `yan wasa hudu ba `yan wasa na sana`a ba ne,sun shiga zagaye na karshe na gasar bayan da suka lashe `yan wasan sana`a da yawa a cikin gasar neman samun iznin shiga gasar karshe.

Mr.Kyi Hla Han,babban manajan gasar yawon kasa kasa ta Asiya ya bayyana cewa,`yan wasa samari ba na sana`a ba daga kasar Sin sun shiga gasar neman samun iznin shiga gasar karshe,wannan ya nuna mana cewa,`yan wasan kasar Sin suna yin kokari.Shahararren `dan wasan kwallon golf na babban yankin kasar Sin Zhang Lianwei shi ma ya shiga wannan gasa,ya gamsar da sakamakon da `yan wasa samari na kasar Sin suka samu,ya ce,  `Wannan shi ne abu mai faranta ran mutane,ana iya cewa,wasan kwallon golf zai samun ci gaba a kasar Sin.`

Budaddiyar gasar wasan kwallon golf ta kasar Sin ba ma kawai ta jawo hankulan mutane masu sha`awar wasan na kasar Sin ba,har ma ta jawo hankulan masu sha`awar wasan na duniya.Kodayake a halin da ake ciki yanzu,wasan kwallon golf na kasar Sin bai samu ci gaba cikin sauri ba,har ma a shiyyar Asiya,ana iya cewa matsayin wasan kwallon golf na kasar Sin yana kama baya,wato cikin dogon lokaci,bai kai matsayi na kasar Korea ta kudu da kasar Indya ba,amma `yan wasan kasar Sin suna yin iyakacin kokari.Game da wannan,babban manajan gasar yawon kasa kasa ta Turai George Oclady ya bayyana cewa, `Daga tarihin wasan kwallon golf na kasar Sin,ana iya gane cewar,kasar Sin ta fara wannan wasa ba da dadewa ba,amma yanzu,`yan wasan kasar Sin sun riga sun nuna karfinsu,wato sun riga sun kai matsayi na `yan wasa daga kasar Korea ta kudu da kasar Indya.Yanzu dai,kamata ya yi a sa kaimi ga `yan wasan kasar Sin da su shiga gasanni iri daban daban,musamman ma su shiga gasannin da za a shirya a kasashen waje.`

Ko shakka babu,ana sa rai kan makomar wasan kwallon golf ta kasar Sin.A hakika dai,yanzu wasan kwallon golf yana kara samun karbuwa a kasar Sin.Mr.Zhang Lianwei yana ganin cewa,idan an kafa wani tsarin horar da yara da samari,to,wasan kwallon golf zai sami ci gaba bisa babban mataki.Ya ce,  `Lallei `yan wasanmu sun riga sun sami ci gaba,amma ya kamata mu kara yin amfani da damar dake gabanmu,mu koyi fasahohin wasa daga wajen `yan wasa na sauran kasashe,na hakake cewa,wasan kwallon golf zai shiga wani sabon mataki ba da dadewa ba.`

Kamar yadda kuka sani,yanzu wasan kwallon golf yana kawo babban tasiri a duk fadin duniya,amma matsayin `yan wasan kasar Sin bai kai matsayin gaba ba tukuna.Ana fatan `yan wasan kwallon golf na kasar Sin za su ci gaba da sanya matukar kokari haka kuma za su nuna babban karfi a cikin gasannin duniya.

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)