Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-24 21:20:32    
Gidan ibada na Yuantongsi

cri

Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. Kamar yadda muka saba yi, da farko dai, za mu karanta muku wasu abubuwa kan wani gidan ibada da ke birnin Kunming, sunansa Yuantongsi, daga bisani kuma, sai wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Titin al'adu na Nanxincang na Beijing'(music)

Gidan ibada na Yuantongsi da aka gina a cikin birnin Kungming na lardin Yunnan shi ne gidan ibada mafi girma a Kunming. An gina shi a matsayin gidan ibada na Butuoluo a gindin babban dutse na Luofengshan a karshen karni na 8 bayan haihuwar Annabi Isa A.S.. Yake-yake nau dogon lokaci sun yi kaca-kaca da wannan gidan ibada a cikin karni na 12. Shi ya sa a shekara ta 1301, aka gina wani sabon gidan ibada mai suna Yuantongsi a asalin wurinsa. An kuma fadada shi a cikin dauloli da dama.

Gidan ibada na Yuantongsi ya yi suna ne saboda kyawawan gine-gine da zane-zane. An gina shi a gangarar babban dutsen. A lokacin da masu yawon shakatawa suke tsayawa a karkashin wata babbar kofa, suna iya ganin kalmomi 'kyawawan wurare masu ni'ima na gidan ibada na Yuantongsi' da aka rubuta a kanta. Daga nan ne masu yawon shakatawa suke iya hangen duk gidan ibada na Yuantongsi.

An shimfida wata babbar hanya zuwa wani babban tabki. Harabar wajen ta fi kama da wani lambu a maimakon wani gidan ibada. A tsakiyar wannan tabki, sai wata rumfa mai hawa 2 da ke da kusurwa 8 da aka gina a zamanin daular Qing. Idan suka kama hanyar da aka gina bisa bankin tabkin, to, masu yawon shakatawa suna iya isa muhimmin gini na wannan gidan ibada, wato muhimmin zaure mai suna Yuantongbaodian. An ajiye mutum-mutumin Buddha na Sanshi a cikinsa, sa'an nan kuma akwai ginshikai 2 da aka sassaka dragons a kansu a cikin muhimmin zauren.

A kololuwar babban dutsen, yana kasacewa da wani duste da aka sassaka kalmomi a kansa, ko da yake ya yi shekara daruruwa yana shan wahalolin iska da ruwan sama, amma ya zuwa yanzu dai yana cikin hali mai kyau, ana iya ganin kalmomin da aka sassaka a kansa sosai.

Bayan wannan muhimmin zauren kuma, an sami kogunan duwatsu 2 masu dogon tarihi, wai su kogunan duwatsu na Yougu da Chaoyin. Akwai almarar cewa, wani dodo ya taba zama a cikin wadannan kogunan duwatsu 2, amma mutanen wurin masu hikima sun kashe shi a karshe. A cikin kogunan duwatsun, an gina wani dakali don horar da wannan dodo.