Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-24 21:10:22    
Ya kamata a kara shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sinadarin calcium kamar yadda ya kamata

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, ya kamata a kara shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sinadarin calcium kamar yadda ya kamata, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan shawarwarin da kwararru da masana na kasar Sin suka bayar kan batun yawan mutane da bunkasuwar kasar Sin. To, yanzu ga bayanin.

Sanin kowa, shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sinadarin calcium zai iya shawo kan cutar kashi da ake kiranta "osteoporosis", amma bayan da masu ilmin kimiyya na kasar Amurka suka gudanar da bincike, sun gano cewa, sinadarin calcium yana taka muhimmiyar rawa ga jikin mutane a fannoni daban daban, shi ya sa shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sinadarin calcium wani abin da ya wajaba ne.

A kwanan nan, kakakin kungiyar kula da abinci ta kasar Amurka kuma kwararriya kan harkokin gina jiki Katharine Talmadge ta bayyana cewa, bincike ya shaida cewa, sinadarin calcium yana iya taimaka wa mutane wajen yin rigakafin sankarar hanji, da sa kaimi ga motsewar tsokan jikin mutane, ciki har da motsewar tsokan zuciya, ta yadda za a iya ba da taimako wajen rage yawan bugun jini da kuma narkar da kitse.

Kuma Madam Talmadge ta ce, Vitamin D wani muhimmin sinadari ne wajen taimaka wa mutane kan karbar sinadarin calcium, amma abinci da yawa ba su kunshe da Vitamin D, shi ya sa ba yadda za a yi, sai matane su rinka samun irin wannan sinadari ta shan hasken rana. Amma abin bakin ciki shi ne, yanzu ba safai mutane su kan yi harkoki a waje ba, kuma idan sun fita daga dakunan, su kan gudu daga hasken rana, wanda ya haddasa ba safai a kan samu isasshen Vitamin D a jikin mutane kamar yadda ya kamata ba, sabo da haka kuma yara masu yawa sun fi saukin kamuwa da cutar laushin kashi.

Ban da wannan kuma Madam Talmadge ta nuna cewa, ko da yake yanzu magungunan ba da kariya ga lafiyar jiki da ke kunshe da sinadarin calcium suna nan iri iri, amma dabara mafi kyau ta shan magungunan da ke kunshe da sinadarin calcium ita ce karbar sinadarin ta abinci. Sabo da haka ya kamata mutane su rinka shan isasshiyar madara ko cin abincin da ke kunshe da sinadarin calcium masu yawa a ko wace rana.

Ma'aikatar amfanin gona ta kasar Amurka ta ba da shawarar cewa, game da mutanen da shekarunsu ya kai 19 zuwa 50 da haihuwa, ya kamata su sami sinadarin calcium na miligram 1000 a ko wace rana, kuma game da matanen da shekarunsu ya zarce 50 da haihuwa, ya kamata su sami sinadarin calcium da ya kai miligram 1200 a ko wace rana.