Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-24 18:28:12    
Sin za ta kara karfin kiyaye hakkin mallakar ilmi

cri

Yau Talata, an yi babban taron dandalin tattaunawar kare hakkin mallakar ilmi a nan birnin Beijing. A gun taron, mataimakiyar firaministan kasar Sin, madam Wu Yi ta yi jawabin cewa, Sin ta rigaya ta mayar da hakkin mallakar ilmi a matsayin wani muhimmin abin da ke cikin karfin takararta, kuma a cikin 'yan shekarun baya, ta sami babban ci gaba a fannin kare hakkin mallakar ilmi. A shekarar da muke ciki kuma, Sin za ta kara daukar matakai masu amfani, don kara karfin kare hakkin mallakar ilmi.

Yawan mahalartan taron dandalin ya zarce 800, ciki har da jami'an sassa da dama na gwamnatin kasar Sin da wakilan kungiyoyin duniya da na shahararrun kamfanonin duniya da kuma na manyan masana'antun gwamnatin kasar Sin da kuma wakilan ofishoshin jakadancin kasashen waje da ke kasar Sin da wakilan masu aikin sa kai kan kare hakkin mallakar ilmi da manema labaru.

A gun taron, Madam Wu Yi, mataimakiyar firaministan kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta mayar da kare hakkin mallakar ilmi a matsayin wata babbar manufarta, ta dauki jerin matakai, ta kuma sami babban ci gaba. An ce, a cikin shekarar bara kadai, Sin ta kwashi ganimar kayayyakin da suka saci fasaha wadanda yawansu ya wuce miliyan 73, bayan haka, yawan darajar kayayyakin shigi da fici da ake satar fasaharsu da tasoshin kwastan na duk fadin kasar suka kwashe ya wuce kudin Sin yuan miliyan 200, kuma kotuna daban daban na kasar sun yanke hukunci kan al'amura fiye da 2000 wadanda ke da hannu cikin keta hakkin mallakar ilmi. Ban da wadannan, Sin ta kuma kafa cibiyoyin kai kara a manyan birane da matsakaita kimanin 50 don kare hakkin mallakar ilmi.

Madam Wu Yi ta bayyana cewa, a shekarar da muke ciki, Sin za ta kara karfin kare hakkin mallakar ilmi, ta ce,"Sin tana ci gaba da daukar babban nauyi a fannin hakkin mallakar ilmi, hakkin mallakar ilmi nata na kanta ba su da yawa, ga shi kuma ba su da karfi sosai a wajen takara, kuma an yi ta samun takaddama ta fuskar hakkin mallakar ilmi, bayan haka, matsalar satar fasaha ta yi tsanani, sabo da haka, gwamnatin kasar Sin za ta kara karfafa niyyarta, za ta kara daukar matakai masu amfani, za ta dinga inganta aikin kare hakkin mallakar ilmi ba tare da kasala ba."

Madam Wu Yi ta kuma yi nuni da cewa, sakamakon ci gaban fasahohin zamani da tasowar tattalin arzikin ilmi da saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya, an daga muhimmancin hakkin mallakar ilmi kwarai da gaske, a sa'i daya kuma, kare hakkin mallakar ilmi ya zama dole ga kasar Sin a wajen kyautata karfinta na yin takara da kasashen duniya. Madam Wu Yi ta kuma yi kira ga kamfanonin kasar Sin da su kara dora muhimmanci a kan hakkin mallakar ilmi, kuma su dauki hakikanan matakai don kare hakkin saura da na kansu.

A cewar shugaban sashen kula da hakkin mallakar ilmi na kungiyar WTO, Adrian Otten, wanda ya halarci taron dandalin, sabo da karuwar karfin kasar Sin a fannin nazari da kirkire-kirkire, duniya da Sin za su amfana gaba daya daga kara karfin kare hakkin mallakar ilmi. Ya ce,"Kare hakkin mallakar ilmi na kasar Sin a kasashen ketare yana ta kara samun muhimmanci. Kayayyakin da Sin ke fitarwa zuwa kasashen waje da hidimar da take samarwa da kuma fasaha, har ma da jarin da kamfanonin Sin suke zubawa a kasashen, Sinawa da kamfanonin kasar Sin suna kara mallakar hakkin mallakar fasahohi nata da kanta, Sin za ta zama cibiyar nazari da kirkire-kirkire ta duniya. Akwai wani ma'aunin da ya shaida wannan batun, wato a cikin shekaru 10 da suka wuce, yawan 'yancin mallakar alama da Sin ta nema a gun ofishin kula da 'yancin mallakar alama da tambari na Amurka ya karu da har ninka sau 15. Sabo da haka, ina fatan Sin za ta kara ganewa cewa, bin yarjejeniyoyin kare hakkin mallakar ilmi da ke shafar WTO, ba ma kawai don sauke alhakin da ke bisa wuyanta da kuma kare hakkin mallakar ilmi na saura ba, haka kuma don kare hakkin mallakar ilmi na kanta."(Lubabatu)