Akwai wasu yara na musamman da ba su son yin magana da mutane, idan an yi musu magan, su kan yi kamar ba su ji ba. Ana kiran wannan halin da suke ciki da suna "cutar kadaici" a fannin ilmin likitanci. A birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin, an kafa wata cibiyar tallafa wa yara domin warkar da wadanda suka kamu da cutar kadaici bisa ilmin kimiyya, ta yadda za su iya sake yin zaman rayuwarsu kamar yadda ya kamata. To, a cikin shirinmu na yau, za mu leke wannan cibiyar tallafa wa yara.
A cikin wani gini da ke gefen babban titin da ke waje da kofar Nanmen ta birnin Tianjin, wakilinmu ya gamu da Guo Jianmei, shugabar cibiyar tallafa wa yara. Madam Guo ba kawai ita ce shugabar cibiyar ba, har ma ita ce mahaifiyar wani yaron da ya kamu da cutar kadaici. Lokacin da wakilinmu ke yin hira da ita, wani kyakkyawan yaro da ke da manyan idanu ya wuce wurin da muke tsayawa a hankali. Madam Guo ta gaya wa wakilinmu cewa, wannan shi ne danta mai suna Xiao An. Nan da nan wakilinmu ya gaisa da shi, amma bai mayar da amsa ba. Madam Guo ta bayyana cewa, wannan ita ce alamar cutar kadaici.
Lokacin da shekarunsa ya kai 3 da haihuwa, an tabbatar da cewa, Xiao An ya kamu da cutar kadaici. Domin warkar da shi, Madam Guo ta yi murabus daga mukaminta domin raka danta zuwan birnin Beijing wajen ganin likita. Kuma lokacin da ake yi wa Xiao An jiyya, Madam Guo ta gamu da iyayen yara masu fama da cutar kadaici da yawa. Kuma dukkansu suna ganin cewa, ba a iya samun hukumomin warkar da cutar kadaici da yawa a kasar Sin ba. Sabo da haka wani irin tunani ya fado mata a zuciya, cewa za ta kafa wata cibiyar tallafa wa yaran da suka kamu da cutar kadaici.
"Dalilin da ya sa ina da wannan tunani shi ne sabo da na farko, hukumomin warkar da cutar kadaici ba su da yawa, mun kwashe lokaci mai tsawo wajen nemansu. Na biyu shi ne sabo da lokacin da aka yi wa dana jiyya, na gano cewa, muddin aka samu dabarar warkar da cutar kadaici, sai a iya tallafa wa yara da kansu. Amma a wancan lokaci, ba a iya samun sauran hukumomin warkar da cutar ba ban da wannan hukumar da ke birnin Beijing, shi ya sa ba yadda za a yi sai yaran da suka kamu da cutar da kuma iyayensu na wurare daban daban sun zo birnin Beijing. Sabo da haka ina ganin cewa, idan ana iya samun irin wannan hukuma a duk fadin kasar Sin, to za a iya rage yawan lokuta da kuma kudaden da iyayen yara suka kashewa wajen ganin likita. "
Bayan da Guo Jianmei ta yi ayyukan share fage a jere, a watan Agusta na shekara ta 2003, cibiyar tallafa wa yara ta birnin Tianjin ta kafu a hukunce. Madam Guo ta bayyana cewa, yanzu an tsara muhimman darusa ne don yaran da shekarunsu ya kai 3 zuwa 12 da haihuwa. Ya zuwa yanzu, wannan cibiyar tallafawa yara tana da malamai da ma'aikata 9, kuma yawan yaran da suka shiga darusan ya kai 50.
Li Yan, wata malamar cibiyar ta gaya wa wakilinmu cewa, su kan kyautata karewar yaran da suka kamu da cutar kadaici wajen yin mu'amala da sauran mutane ta yin amfani da ilmin hankalin mutane, amma a kan bukaci dogon lokaci wajen ganin ci gabansu kadan. Kuma bisa matsayinta na wata malama, ta kan bukaci yin hakuri sosai. A waje daya kuma, sabo da wadannan yara ba su iya sarrafa aikace-aikacensu kamar yadda ya kamata, shi ya sa malamai su kan ji rauni kusan a ko wace rana. Kuma Li Yan ta kara da cewa, "Wata rana, wani yaro yana farin ciki yana wasa, kuma ina cin abinci, shi ya sa ban yi shirin kare kaina ba. Amma abin bakin ciki ya faru, wancan yaro ya cije ni ba zato ba tsammani, amma a wancan lokaci, ban iya mayar da martani sosai kan batun ba. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da idan na mayar da martani sosai kan wannan batun da ya yi, to zai sake yinsa a nan gaba. Shi ya sa ba yadda za a yi sai na kyale shi kamar bai taba cizo na ba."
Ban da malaman da suke aiki a cibiyar tallafa wa yara, kullum masu sa kai su kan zo cibiyar domin yin wasa tare da wadannan yara. Zhang Shun mai shekaru 20 da haihuwa shi ne wani ma'aikaci wajen sayar da tufafi. Bayan da ya san cutar da wadannan yara suka kamu a watan Oktoba na shekarar da ta gabata, har kullum ya kan zo cibiyar a ran talata da kuma juma'a da yamma na ko wane mako. Lokacin da Zhang Shun ya tabo magana kan wadannan yara, ya bayyana cewa, "Ina zuwa cibiyar a ko wane mako domin yin wasa tare da wadannan yara. Lokacin da na ga sun yi murmushi a gabana, sai na ji farin ciki sosai kamar na zuba ruwa a kasa na sha."
Iyayen yaran da suka kamu da cutar kadaici da kuma ma'aikatar cibiyar tallafa wa yara sun samu goyon baya sosai sakamakon zuwan masu aikin sa kai. A waje daya kuma wasu kungiyoyin fararen hula su kan samar da taimako ga cibiyar wajen kayayyakin ayyukan koyarwa, ta yadda za a iya gudanar da ayyukan cibiyar sosai. Kande Gao)
|