Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-23 18:59:10    
Takaitaccen bayani game da kabilar She

cri

Kabilar She tana daya daga cikin kabilun da da su da yawan mutane sosai. Suna zama a yankunan lardin Fujian da na Jiangxi da Zhejiang da Guangdong da na Anhui. Amma galibinsu suna da zama a yankunan da ke bakin tsaunuka a lardunan Fujian da Zhejiang. 'Yan kabilar suna kiran kansu "Mutanen bakin tsaunuka". Bisa kididdigar da aka yi a duk fadin kasar Sin a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar ya kai fiye da dubu dari 7, kuma suna amfani da yarensu, amma galibinsu sun iya harshen Han.

Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, 'yan kabilar She suna cikin zaman al'ummar kama karya. Tattalin arziki da zaman al'umma da al'adunsu sun samu cigaba sannu a hankali kuma cikin hali maras daidaito. Muhimmiyar sana'ar da 'yan kabilar suka yi ita ce aikin gona da sana'ar farauta. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, an kafa kananan gwamnatocin kabilar She 57 a yankunan da 'yan kabilar suke da zama. Bayan da aka yi gyare-gyare kan zaman al'ummar kabilar She kamar yadda aka yi a duk fadin kasar Sin, jama'ar kabilar She sun samu gonaki da filayen shuka itatuwan shayi da gandun daji. A cikin 'yan shekarun na da suka wuce, masana'antun da ke lardin Fujian da na Zhejiang sun samu cigaba sosai. Makomar tattalin arzikin yankunan kabilar tana da haske kwarai.

'Yan kabilar She sun fi son rera wakoki lokacin da suke aiki. Suna rera irin wadannan wakoki ne da yarensu.

A waje daya kuma, matan kabilar She wadanda suke kokarin aiki ba ma kawai sun kware kan aikin gona ba, har ma sun kware kan sana'ar hannu. Kayayyakin da suke sakawa yanzu sun riga sun zama kayayyakin da masu yawon shakatawa suke son saya lokacin da suke shan iska a yankunan kabilar.

Bugu da kari kuma, jama'ar kabilar She suna son motsa jiki, alal misali hau kan dutse da doki da sauran gasanni iri iri.

A kan tarihi, 'yan kabilar She su kan yi kaura, sabo da haka, 'yan kabilar sun saba da zama a cikin bukoki da gidajen da aka gina da katako. Amma yanzu, ingancin zaman rayuwar 'yan kabilar She ya samu kyautatuwa sosai. Mutane da yawa suna gina gidajensu da benaye hawa biyu. Lokacin da ake lokacin sanyi, iyalai su kan zauna bakin wuta domin dumama jikinsu.

Bisa al'adar kabilar She, kowane saurayi yana auren mace daya. Idan wani saurayi da wata mace suna da sunan kaka daya, shi ke nan, ba su yi aure ba. Matasa suna da 'yancin neman soyayya. Su kan rera wa juna wakoki iri iri domin neman soyayya. (Sanusi Chen)