Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-23 18:59:37    
Nuri al-maliki yana share fage domin kiran taron kasa da kasa kan batun tsaron kasar Iraki

cri

Ran 22 ga wata, Nuri al-maliki, firayim ministan kasar Iraki ya sauka birnin Alkahira, hedkwatar kasar Masar don fara yin ziyararsa ta karo na farko a kasar Masar tun bayan da ya zama firayim minista. Babban makasudin ziyararsa shi ne, domin share fage ga taron kasa da kasa a kan batun tsaron kasar Iraki da za a shirya a Sharm el-Sheikh na kasar Masar a farkon watan gobe. Ban da kasar Masar, Maliki zai kai ziyara a Saudi Arabiya da Kuwait da hadaddiyar daular Larabawa da Oman da dai sauran kasashen yankin Gulf.

A ran 3 da ran 4 ga watan gobe, a birnin Sharm el-Sheikh na kasar Masar, za a shirya taron ministoci da zaunannun kasashe biyar na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashe 8 wato G8 da kasashe da ke makwabtaka da kasar Iraki za su halarta. Inda za a nemi hanyar da za a bi wajen kawo karshen tashe-tashen hankula da ke haddasa zuba jini a kasar Iraki. Sabo da haka yayin da Maliki ke yi shawarwari a tsakaninsa da Hosni Mubarak, shugaban kasar Masar da Ahmed Nazif, firayim ministan kasar a wannan rana a birnin Alkahira, dole ne, halin zaman lafiya da ake ciki yanzu a kasar Iraki ya zama wani babban batu da suka yi shawarwari a kai. A gun taron manema labaru da aka shirya bayan shawarwari da aka yi a tsakaninsa da Nazif, Maliki ya bayyana cewa, duk hargitsin nuna karfin tuwa da ake yi yanzu a kasar Iraki, aikace-aikace ne da kungiyar Al-Qaeda da mabiyanta suka yi. Yanzau, an riga an sassauta hargitsin sosai da ake yi a tsakanin musulmi masu dirikar Sunni da Shi'ite a kasar Iraki. Daga wajensa, Nazif ya ce, gwamnatin kasar Masar tana nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Iraki bisa kokari da take yi wajen tabbatar da jituwa a tsakanin rukunonin addini daban daban da bangarorin jama'ar kasar Iraki, sa'an nan tana Allah wadai da duk ta'addanci da ake yi wa fararen hula ta hanyoyi daban daban.

Ka zalika kyautata hulda da ke tsakanin kasashen Iraki da Masar wani babban batu ne daban da kasashen biyu ke yin shawarwari a kai. Tun bayan da gwamnatin musulmi mai darikar Shi'ite wadda ke karkashin shugabancin Maliki ta fara gudanar da harkokin mulki, hargitsin da ake yi a tsakanin musulmi masu darikar Sunni da Shi'ite ya yi ta hauhawa a kasar Iraki, sabo da haka kasashe da ke makwabtaka da kasar Iraki suna nuna damuwa ga irin barazana da ake kai wa zaman lafiya da zaman karko na yankin gabas ta tsakiya ta hanyar kara tabarbarewar halin tsaro da ake ciki a kasar Iraki, dadin dadawa kasar Masar ta fi mai da hankali ga tasirin da halin nan ke kawo wa hulda a tsakanin kasashen Masar da Iraki. Sabo da haka bayan da ya yi shawarwari a tsakaninsa da shugaba Mubarak da Nazfi bi da bi, sai Maliki ya bayyana cewa, shi da shugaba Mubarak sun yi shawarwari a kan duk matsaloli da ke hana bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu, kuma suna ganin cewa, ya kamata, su kara kokari wajen sa kaimi ga yalwata hulda a tsakanin kasashensu biyu, sa'an nan kamata ya yi, su kara inganta huldar. Daga wajensa, Nazif ya ce, ziyarar da Maliki ke yi a wannan gami za ta kara sa kaimi ga bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen Masar da Iraki. Kuma ya sha bayyana matsayin kasarsa a fili kan nuna cikakken goyon baya ga tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar Iraki. Bayan shawarwarin da suka yi a wannan rana, Maliki da Nazfi gaba daya sun bayyana cewa, su goyi bayan kamfanonin kasar Masar da su koma kasar Iraki, don shiga ayyukan sake gina kasar Iraki bayan yakin.

Manazarta suna ganin cewa, kara tabarbarewar halin tsaro da ake ciki a kasar Iraki da kara hauhawar hargitsin da ake yi a tsakanin musulmi masu bin darikoki daban daban da ta'addanci da ake nunawa da karfin tuwo sun riga sun kawo barzana mai tsanani ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da zaman karko a kasashe da ke makwabtaka da kasar Iran da kuma duk yankin gabas ta tsakiya. Yaya za a yi a taimaki kasar Iraki wajen kawo karshen hargitsin zuba jini a kasar Iraki tun da wuri da sake samar da zaman lafiya a kasar Iraki yadda ya kamata. Wannan ya riga ya zama ra'ayi bai daya da gamayyar kasa da kasa ta samu. Ziyarar da Maliki ke yi a kasashen Larabawa za ta yi taka rawa sosai wajen kyautata halin tsaro a kasar Iraki. (Halilu)