Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-20 19:53:52    
Tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kashi 11.1% a cikin farkon watanni uku

cri
Tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da bunkasa cikin sauri, bayan da ya tabbatar da samun saurin karuwa da fiye da kashi 10% a shekaru hudu a jere. A cikin farkon watanni uku na wannan shekara, yawan tattalin arzikin kasar Sin ya kai kudin Sin yuan biliyan 5028 da miliyan 700, wanda ya karu da kashi 11.1%, kuma saurin karuwar ya kai kashi 0.7% bisa na makamancin lokaci na shekarar da ta wuce. Jiya kakakin hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin, malam Li Xiaochao ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana gudana yadda ya kamata, amma duk da haka, matsin da yake fuskanta a fannin hauhawar farashin kaya ya karu, kuma akwai hadarin kai wani matsayin koli fiye da kima.

A gun taron manema labaru da aka yi a jiya Alhamis, kakakin hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin, malam Li Xiaochao ya ce,"A cikin farkon watanni uku, saurin bunkasuwar tattakin arzikin kasar Sin ya karu sakamakon zuba jari da sayen kayayyaki da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da aka yi. Saurin karuwar kayayyakin kiri da aka sayar ya karu da kashi 2.1% bisa na makamancin lokaci na shekarar bara, a yayin da saurin karuwar jarin da aka zuba wajen samar da kadarori ya ragu da kashi 4%. A sa'in da saurin zuba jari ya ragu, sayen kayayyaki da kuma shigowa da kayayyaki da fitar da su sun karu cikin sauri, wadanda ba ma kawai suka sassauta raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki da mai yiwuwa ne za a samu sakamakon raguwar saurin zuba jari da aka yi ba, hatta ma ya kara kawo wasu bukatu."

Adadin da hukumar ta bayar ya kuma yi nuni da cewa, a cikin farkon watanni uku, yawan kudin shiga da mazauna birane da kauyuka na kasar Sin suka samu ya karu kwarai, musamman ma yawan karuwar kudin shiga na manoma ya kai wani matsayin koli yau da shekaru goma da suka wuce. Sakamakon hakan kuma, mazaunan kasar Sin sun kara sha'awar sayen kayayyaki, har ma a cikin farkon watanni uku, yawan kayayyakin kiri da aka sayar ya zarce kudin Sin yuan biliyan dubu 2, wanda ya karu da kusan rabi bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Amma a hannu daya kuma, a cikin farkon watanni uku, yawan hauhawar farashin kayayyaki ya karu, wanda ya karu da kashi 2.7% bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Game da wannan, malam Li Xiaochao ya ce, farashin kayayyaki ya taso ne sakamakon hauhawar farashin abinci, idan an janye dalilin, to, hakika yawan hauhawar farashi ya kai kashi 1.2% ne kawai, wanda ya zo daidai da na shekarar da ta wuce. Amma a sa'i daya, ya kuma bayyana cewa, sakamakon dalilai da dama, matsin da Sin ke fuskanta a fannin hauhawar farashin kaya yana karuwa. Ya ce,"babban dalilin da ya haddasa hauhawar farashin kaya a yanzu shi ne karuwar farashin abinci, da zarar yanayi ya kawo wa abinci da aikin noma tasiri, to, abin zai haddasa hauhawar farashin kaya. A shekarar da muke ciki, za mu kara gyaran tsarin tsai da farashin albarkatun kasa, wanda zai haifar da karuwar farashin ruwa da gas da sauransu. Bayan haka, a kasuwar duniya, farashin tagulla da gorar ruwa da takin zamani da dai sauran danyun kayayyaki yana karuwa sosai, kuma Sin tana shigowa da dimbin kayayyakin, sabo da haka, suna kawo wa CPI matsi, wato farashin kayayyakin da mazauna ke saye."

Malam Li Xiaochao ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai a kan kasancewar wasu matsaloli ta fuskar tattalin arziki. Ya ce,"yanzu ana gudanar da tattalin arziki cikin sauri kuma yadda ya kamata, amma idan saurin bunkasuwar tattalin arziki ya ci gaba da karuwa, to, mai yiwuwa ne saurin zai kai wani matsayin koli na fiye da kima, sabo da haka, za mu kara mai da hankali kan saurin bunkasuwar tattalin arziki da rarar kudin ciniki ya haddasa, kuma za mu mai da hankali kan tsarin tattalin arziki."