Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-20 15:58:09    
Za a gudanar da jerin gasannin gwaje-gwaje domin taron wasannin Olympic na Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, kuna sane da, cewa akan yi atisaye sau da dama kafin a nuna wasannin fasaha masu ban sha'awa domin cimma burin 'yan kallo. Haka kuma kafin a gudanar da kowane gagarumin taron wasannin Olympic, kasa mai masaukin taron takan shirya jerin gasannin gwaje-gwaje na wasannin Olympic domin jarraba ayyukan share fage daga dukan fannoni da kuma filaye da dakunan wasannin motsa jiki na mai masaukin taron. Wakilinmu ya samu labari daga kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing, cewa tun daga watan Yuli na wannan shekara, za a gudanar da gasannin gwaje-gwaje sama da 40 bi da bi domin taron wasannin Olympic na Beijing. An lakaba wa wadannan gasanni cewa " Beijing mai sa'a", wadanda suka kasance tamkar wani atisaye ne da za a yi na taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

An shirya wani taron ganawa da manema labaru dangane da wadannan gasannin gwaje-gwaje ne a cibiyar watsa labarai ta taron wasannin Olympic na Beijing, inda Mr. Yang Shuan, mataimakin shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya yi bayani kan ayyukan share fage da ake yi ga yin jerin gasannin gwaje-gwaje. Mr.Yang ya jaddada, cewa shekarar 2007, wata muhimmiyar shekara ce ta share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing. Shekarar bana, a galibi dai, za a kammala ayyukan share fage iri daban-daban na taron wasannin Olympic na Beijing. Bayan haka, za a yi gwaje-gwaje taki kan taki ga filaye da dakunan gasanni da ba na gasanni ba na taron wasannin Olympic. Ko shakka babu ma'aikata da mutane masu aikin sa kai da suka shiga cikin kungiyoyin kula da harkokin taron wasannin Olympic za su samu horo mai kyau. Saboda haka, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing yake mai da hankali sosai kan wadannan gasannin gwaje-gwaje da za a gudanar a jere.

Mr. Yang Shuan ya furta, cewa ' Mun rigaya mun tabbatar da ajandar dukan gasanni yayin da muka tabbatar da lokacin yin gasanni, da filaye da dakunan yin gasa; Ban da wannan kuma, ana nan ana gaggauta share fage ga yadda za a gudanar da gasanni, da aikin gina filaye da dakunan da abun ya shafa daidai bisa ajandar da aka tsara; Kazalika, yanzu ana uyin shiri sosai wajen karbar 'yan wasa,da sama da otel-otel da dai sauransu. Dadin dadawa, kwamitocin shirya gasanni daban-daban dukansu suna aikin fitar da shirye-shiryen da abun ya shafa, wadanda suka samu amincewa daga kowace hadaddiyar kungiyar wasan motsa jiki ta kasa da kasa.

An bayyana cewa, jerin gasanni dake da lakabin " Beijing mai sa'a" da za a gudanar sun hada da ayyukan wasa guda 28 na taron wasannin Olympic na yanayin zafi da kuma ayyukan wasa guda 2 na taron wasannin Olympic na nakasassu na yanayin zafi, wato gasanni 42 ke nan za a gudanar da su cikin yin amfani da filaye da dakuna na yin gasa da kuma horaswa domin taron wasannin Olympic da na nakasassu na Beijing. Lallai wannan zai samar da kyakkyawar damar yin atisaye da aka samu ba da sauki ba ga aikin shirye-shiryen taron wasannin Olympic na Beijing. Gasanni 26 daga cikinsu ,za a gudanar da su ne a shekarar da muke ciki.

'Wadannan gasanni da za a gudanar za su dauki dogon lokaci', in ji Mr. Yang Shuan, ' Ba ma kawai za a yi wadannan gasanni cikin yin amfani da da filaye da dakuna na taron wasannin Olympic na Beijing ba, har ma za a yi amfani da na'urorin kidayar lokaci da kuma maki da dai sauran makamantansu na gagarumin taron wasannin Olympic na Beijng'.

Sa'annan Mr. Yang ya fadi, cewa idan ana so a gudanar da wata gasar wasan motsa jiki musamman ma taron wasannin Olympic, to wani muhimmin aikin da ya kamata a yi, shi ne tsara wasu shirye-shiryen shawo kan matsalolin ba-zata. Wasu maganganu da mai yiwuwa ne za a gamu da su a lokacin da ake yin gasannin gwaje-gwaje na ' Beijing mai sa'a ' , ko shakka babu za su bada taimako ga kyautata shirye-shiryen magance matsalolin ba-zata na taron wasannin Olympic na Beijing ; Haka kuma za su janyo tasiri mai kyau ga gudanar da wannan gagumin taro lami-lafiya.

Ko da yake an mayar da wadannan gasanni na ' Beijing mai sa'a ' a matsayin atisaye da za a yi daga dukan fannoni domin taron wasannin Olympic na Beijing, amma duk da haka, ya kasance da bambanci na ainihi tsakaninsu da taron wasannin Olympic na Beijing.

A karshe dai, Mr.Yang Shuan ya yi fatan da'irori daban-daban na zamantakewar al'ummar kasar za su nuna himma da goyon baya ga wadannan gasannin gwaje-gwaje.( Sani Wang )