|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2007-04-19 18:52:41
|
|
Kasar Sin tana fata bangarori daban daban da ke da nasaba da batun Darfur za su dauki matakai masu yawa bisa manyan tsare-tsare
cri
Yau 19 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Liu Jianchao ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, kan batun shiyyar Darfur ta kasar Sudan, ya kamata bangarori daban daban da abin ya shafa su dauki matakai masu yawa bisa manyan tsare-tsare, amma ba tattauna kan sanya takunkumi ba. Kasar Sin tana fata za a tabbatar da ra'ayi daya da bangarori daban daban suka samu tun da wuri.
A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, Mr. Liu Jianchao ya ce, kwanan baya, gwamnatin kasar Sudan ta amince da shiri na mataki na biyu a duk fannoni dangane da girke sojojin hadin kan M.D.D. da kungiyar tarayyar kasashen Afrika, wato kungiyar AU a shiyyar Darfur, wannan shi ne wani ci gaba mai kyau da aka samu. A wannan lokacin da aka samu ci gaba kan batun Darfur, ya kamata banagrori daban daban su dauki matakai masu yawa bisa manyan tsare-tsare, domin sa kaimi ga tabbatar da ra'ayi daya da abin ya shafa da aka samu. (Bilkisu)
|
|
|