Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-18 18:26:56    
Tabbatar da samun bunkasuwa muhimmiyar hanya ce da ake bi wajen daidaita batun Darfur na Sudan

cri

A 'yan shekarun baya dai, batun Darfur ya fi janyo hankulan gamayyar kasa da kasa. To, mene ne ainihin batun Darfur? Wace hanya ce da ya kamata a bi wajen daidaita shi? Kuma wace irin rawa ce da ya kamata gamayyar kasa da kasa su taka kan wannan batu? Wakiliyarmu ta ziyarci Madam He Wenping, daraktar ofishin nazarin harkokin Afrika na Kolejin nazarin harkokin Yammacin Asiya da na Afrika na kasar Sin don jin ta bakinta a game da wannan batu. Madam He Wenping ta fadi cewa:

" Idan an duba wannan batu daga fuska, to an yi hasashen cewa ainihin batun Darfur shi ne wata magana ce ta arangamar tsakanin kabilu na kasar. Amma a zahiri dai, wata magana ce ta bunkasuwa.".

Sa'annan Madam He ta bayyana, cewa kasar Sudan ta samu dan ci gaban tattalin arziki sakamakon samun riba daga mai ; amma kuwa, jama'ar yankin Darfur ba su ci gajiya ba har sun kara koma baya idan an kwatanta su da na sauran yankunan kasar. Da yake ainihin batun Darfur shi ne maganar bunkasuwa, shi ya sa ake kokarin gano bakin zaren da ya dace da daidaita shi. A ganin Madam He Wenping, wata hanya mafi kyau da ya kamata a bi wajen daidaita wannan batu, ita ce shawarwari guda hudu da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya gabatar yayin da ya kai ziyara a kasar Sudan a shekarar da muke ciki,wato ke nan ya kamata a girmama mulkin kai da cikakken yankin kasa na Sudan, da daidaita wannan batu ta hanyar yin shawarwari ; shawara ta uku, ita ce ya kamata Majalisar Dinkin Duniya da sojojin kungiyar tarayyar Afrika wato AU su sanya kokari tare don daidaita batun ; Shawara ta hudu ita ce, ya kamata a kiyaye zama mai dorewa na yankin Darfur da kuma kyautata zaman rayuwar jama'ar wurin.

Madam He Wenping ta kara da, cewa lallai kasar Sin ta dauki matakai masu yakini game da wannan fanni. A lokacin da shugaba Hu Jintao yake yin ziyara a kasar Sudan, ya shelanta cewa kasar Sin za ta kara samar wa jama'ar yankin Darfur taimakon kayayayki kai tsaye, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin Yuan miliyan 40. A lokaci daya kuma, Madam He ta jaddada, cewa ya kamata gamayyar kasa da kasa su ma su kara tallafa musu. Ta furta, cewa: ' Ya kamata gamayyar kasa da kasa su bai wa jama'r yankin Darfur taimakon ko kayayyaki ko kuma kudi tsaba,ta yadda za a kyautata zaman rayuwarsu da kuma zaunar da gindin kasar Sudan. Hakan zai kara daukaka ci gaban yunkurin gudanar da harkokin siyasa'.

Kazalika, Madam He Wenping ta taba magana kan kalamomin da wata kasa da wata kungiya suka yi cewar wai ya kamata a garkama wa Sudan takunkumi. A ganin Madam He, kakaba takunkumi, ba hanya ce mai kyau da ake bi wajen daidaita batun Darfur domin muddin an yi haka, to labuddah jama'ar Sudan su ne za su fi shan masifa. Madam He ta ce, wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin take jaddada har kullm a kan cewa ya kamata a bi hanyar zaman lafiya, da shawarwari da kuma ta diplomasiyya wajen daidaita wannan batu. Amma, ra'ayoyi da matakai da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun samu wani irin martani maras kyau da wasu kasashen duniya suka bayar a kan cewar wai kasar Sin ba ta dauki alhakin dake bisa kanta ba har ta kara hura wutar rikicin da ake yi a yankin Darfur. Madam He ta yi Allah wadai da wadannan sambatun banza. Ta fadi cewa: "Lallai har ila yau dai wadannan kasashe suna da ra'ayi irin na cacar baki. Ruwa a jallo ne suke zargin komai da komai da kasar Sin take yi. A zahiri dai, kamar yadda gwamnan jihar Kudancin Darfur ya fada cewa hanya ce daya tak da ya kamata a bi wajen kawar da sanadin haifar da rikicin, ita ce bunkasa tattalin arziki, da raya muhimman ayyuka da kuma kyautata tsarin kiwon lafiya da na ilmantarwa da dai sauran ayyukan hidimomin zamantakewar al'ummar kasar. Ya kuma ce, abun ya zama dole wasu kasashe su kara yin abubuwan da jama'ar Sudan suke bukata maimakon nuna musu yatsa ba gaira ba dalili da wanke hannu daga alhakinsu. ( Sani Wang )