Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-18 15:18:37    
Wasanni a kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Iro Bambale, mazaunin garin Zaria, jihar Kaduna da ke tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya turo mana, ya tambaye mu, wace harkar wasa ce ta fi shahara a kasar Sin? Wadanne nau'o'in wasanni ne aka kirkiro su a kasar Sin, sa'an nan duniya ko kungiyar wasannin Olympics ta duniya ta ara ta yadda a ci gaba da yinsa a wasannin duniya? To, hakika, mutanen Sin suna son wasanni iri iri, kuma gwamnatin kasar tana mai da hankali sosai a kan bunkasa harkokin wasanni, yanzu bari in dan bayyana muku yadda harkokin wasanni suke a kasar Sin.

A shekarar 1995, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da "tsarin shirye-shiryen wasannin motsa jiki a tsakanin dukan jama'a". Burin wannan shiri na tsawon shekaru 15 shi ne kafa wani tsari na samar da wasannin motsa jiki ga dukan jama'ar kasar Sin. A halin yanzu dai, akwai gidajen wasanni da filayen wasanni da yawansu ya zarce dubu 616 a duk fadin kasar Sin, kuma yawancinsu a bude suke ga al'umma baki daya. Bayan haka, a gundumomi da lambunan shan iska da gefunan hanyoyi na birane daban daban, a kan gina filayen wasanni da aka harhada su da na'urorin wasanni, wadanda kuma suka samar da saukin wasanni ga jama'a. Bayan haka, gwamnatin kasar Sin ta kuma zuba makuden kudaden jari a wajen bunkasa harkokin wasanni. Kawo karshen shekarar 2003, yawan kudaden jarin da babbar hukumar kula da harkokin wasanni ta kasar Sin ta zuba ta fuskar aiwatar da shirin wasannin motsa jiki a tsakanin dukan jama'a ya riga ta kai kudin Sin yuan biliyan daya.

Bunkasuwar harkokin wasanni a tsakanin dukan jama'a ta kuma kawo wa jama'ar Sin sauye-sauyen ra'ayoyi dangane da zaman rayuwa. Jama'a suna kokarin yin wasanni iri iri, don inganta lafiyar jikinsu da kyautata zaman rayuwarsu. Wasu sabbin wasanni, kamar su hawan tsauni da tseren dawaki da wasan kwallon golf da wasan kwallon bowling da wasan Yoga da sauransu suna samun karbuwa sosai, musamman ma a tsakanin matasa.

Ban da wasannin yau da kullum, Sinawa suna kuma kokarin shiga gasanni iri iri a duniya. A watan Maris na shekarar 1959, malam Rong Guotuan, wato dan wasan Pingpong na kasar Sin, ya zama zakara a gasar cin kofin duniya ta wasan Pingpong, hakan nan kuma ya kasance zakaran duniya na farko a tarihin kasar Sin. Daga bisani kuma, Sin ta samu dimbin nasarori a bangaren wasanni iri iri. Ya zuwa shekarar 2003, gaba daya 'yan wasanni na kasar Sin sun sami lambobin zinari na duniya har 1695, a yayin da suka karya matsayin bajinta na duniya har sau 1106.

A nan kasar Sin, akwai kuma wasannin gargajiya iri iri da Sinawa ke yi tun da can, kamar su wasan Kungfu da wasan Taichi da wasan Qigong da darar kasar Sin da dai sauransu. Wadannan wasanni ba ma kawai suna samun karbuwa a tsakanin Sinawa ba, har ma suna ta samun karbuwa a kasashen duniya baki daya. Kamar yadda kowa ya sani, Sin tana daukar nauyin shirya wasannin Olympics a shekarar 2008 wadda ke zuwa, kuma a gun wani taron manema labaru kan bikin wasan Kungfu na duniya na karo na biyu wanda aka shirya a watan Disamba na shekarar da ta gabata a birnin Zhengzhou na kasar Sin, wani jami'in bangaren shirya bikin ya fayyace cewa, hukumar kula da wasannin Olympics na duniya ta riga ta amince da wasan Kungfu a matsayin wasa amma a bayan fage. Sabo da haka, karo na farko ne wasan Kungfu zai fito a gun wasannin Olympics a shekarar 2008 a nan birnin Beijing. Gaskiya wannan labari ne mai faranta rai, muna kuma fatan ta kafar wasannin Olympics, wasannin gargajiya na al'ummar kasar Sin da dai sauran harkokin wasannin kasar za su iya kara bunkasa.(Lubabatu)