Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-18 14:53:00    
Masana'antun yin kayayyakin al'adu na kasar Sin suna kara samun bunkasuwa

cri

Tun daga shekarar 2000 har zuwa yanzu, masana'antun yin kayayyakin al'adu na kasar Sin sun sami bunkasuwa da saurin gaske, gwamnatin tsakiya bi da bi ne ta bayar da manufofi masu sanya kwarin guiwa da yawa, kuma masana'antun yin kayayyakin al'adu suna kara karuwa da sauri, A duk kasar Sin, an kafa yankunan musamman da ke kunshe da masana'antun yin kayayyakin al'adu masu sabbin samfurori da yawa a larduna da jihohi da yawa.

Mataimakin direktan sansanin yin nazari kan raya da kuma kago sabbin kayayyakin al'adu na kasar Sin wato shehun malami Chen Shaofeng ya gaya wa manema labaru cewa, a wurare daban daban na kasar Sin, an kafa masana'antun yin kayayyakin al'adu da yawa, amma idan ba a mai da hankali sosai ga tsara fasalinsu ba, to mai yiyuwa ne bunkasuwar da aka samu ba za ta iya zama gaskiya ba. Ya bayyana cewa, na ba da shawara cewa, idan gwamnatiocin kananan hukumomi suna son tsara fasalin yankunan musamman da ke kunshe da masana'antun yin kayayyakin al'adu tare da masana'antu da rukunonin masu fasaha, to ya kamata su hada da ayyukan fitar da kayayyakin al'adu da koyon abin da suke bukata da yin nazari gu daya, wato ya kamata su tsara fasalin yankunan musamman na fitar da kayayyakin al'adu da sa kaimi ga raya su bisa tushen samun fahimtar juna a tsakaninsu. Bisa sakamakon nan ne za a iya daidaita matsalolin da ake gamuwa a lokacin samun bunkasuwa da kuma kawar da bunkasuwar bogi .

Wani babban jami'in lardin Guizhou na kasar Sin mai suna Wang Fuyu ya bayyana cewa, lardin Guizhou ya iya bin hanyarta ta kanta da ke da halayen musamman wajen fitar da kayayyakin al'adu. Ya bayyana cewa, Lardin Guizhou lardi ne da ke da kabilu da yawa, yana da wadatattun albarkattun kayayyakin al'adun gargajiya na kabilu daban daban. Wato yana da kabilar Miao da Buyi da Dong da Hui da sauran kananan kabilu 13 tare da wasu al'umman da suke zama a wurin tun kakani-kakaninsu , lardin shi ne babban iyalin da ke da kabilu da yawa wadanda suke zama cikin jituwa sosai, a cikinsu, da akwai sigar al'adu iri iri da yawa tare da abubuwan gargajiya irin na al'adu da kuma tsohon al'adun da ba a taba gyara su ba na zamani aru aru, har da rukunonin gine-ginen gargajiya da sutura da harsuna da bukukuwa da al'ada da abinci da auren gargajiya da wake-wake da kide-kide na gargajiya da dai sauransu, kai, suna da yawan gaske, kuma an kiyaye su da kyau sosai, suna da daraja sosai wajen al'adu.

Mataimakin shugaban kolejin yin nazari kan fitar da kayayyakin al'adu na jami'ar Beijing Mr Xiang Yong ya bayyana cewa, horar da jami'an kula da harkokin al'adu na wuri wuri na da ma'ana mai muhimmanci sosai wajen raya kayayyakin al'adu. Ya bayyana cewa, daga cikin ayyukan tsara fasali da muka yi, da farko ya kamata mu yi aikin ba da horo, muna fatan manyan sassan da abin ya shafa da manyan shugabanninmu za su sami wani ra'ayin gaskiya a kan masana'antun yin kayayyakin al'adu, da kuma aiwatar da harkokinsu bisa wannan ra'ayin. Mu iya tsara wasu darusa don nuna fata ga gwamnati da ta fahimci cewa, da akwai bambanci a tsakanin aikin raya kayayyakin al'adu da tsohon ra'ayinsu dangane da al'adu, ta hakan, za mu iya fahimta cewa, a lokacin da muke tsara fasalin ko muke ba da horo, har lokacin da muke sa kaimi ga raya kayayyakin al'adu na wuri wuri, za mu iya fahimta cewa, za a iya ba da hakikanin taimako a fannin nan.

Kafin wasu watannin da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta bayar da babban tsari na shekaru biyar masu zuwa na raya kayayyakin al'adu, inda ta karfafa kara saurin raya masana'antun yin kayayyakin al'adu. An amince cewa, a cikin 'yan shekaru masu zuwa, sansanoni da masana'antun yin kayayyakin al'adu na kasar Sin za su kara girma wajen samun sakamako da kuma daukar matakai tare da rayuwa sosai.(Halima)