Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-18 13:08:12    
An dauki matakai don yin kokarin yaki da talaucin birane

cri
A ran 16 ga wata, a babbar hukumar gidajen kwana da ke birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, an kira taro na 21 na majalisar hukumar gidajen kwana ta M.D.D. A gun taron, wakilan da suka zo daga kasashe mambobi 58 na majalisar da na wasu kungiyoyin kasashen duniya da na shiyya-shiyya za su tattauna matsalolin raya birane har zuwa dogon lokaci, da yaki da talauci da kyautata ingancin zaman rayuwar jama'a. To, jama'a, masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilansu suna ruwaito mana daga wajen taron.

An shafe kwanaki 5 ana yin wannan taro, babban batun wannan taro shi ne "A raya birane har zuwa dogon lokaci, kuma a mai da muhimmanci wajen daukar matakai domin yaki da talauci wajen kudi da yin safiyo". Madam Anna Tibaijuka, mataimakiyar babban sakataren M.D.D. kuma direktar zartaswa ta hukumar gidajen kwana ta yi jawabi a gun bikin bude taro inda ta ce, "An kira taro na 21 na majalisar hukumar gidajen kwana ne a daidai muhimmin lokacin tarihi. Daga shekarar 2007, 'yan adam za su zama mutanen birane, sabo da daga yanzu yawancin mutane za su yi zaman rayuwarsu cikin birane, amma ba kauyuka ba, irin wannan yunkurin sauyawar mutane ba ya juyuwa baya."

Daidai kamar yadda madam Tibaijuka ta fada cewa, dalilin da ya sa karuwar yawan gidajen talakawa ya zo daga fannoni da yawa, ciki har da shigowar yawan manoma 'yan kwadago cikin birane, karuwar yawan marasa aikin yi, kuma karancin kudin da gwamnatin da sassan kasuwanci suka ware domin gina gidajen talakawa.

Domin daidaita wadannan matsalolin da aka ambata a baya, wasu kasashe sun riga sun dauki matakai masu yakini. A gun bikin bude taron, Mr. Mwai Kibaki, shugaban kasar Kenya ya yi bayani ga wakilai masu halartar taro kan shirin da kasar Kenya ta dauka wajen kyautata unguwannin talakawa. Ya ce, "Bisa taimakon hukumar gidajen kwana da sauran abokan gama gwiwa, gwamnatin Kenya ta riga ta dauki matakai da yawa don yin gaba da kalubale da aka yi mata sabo da wadannan matsaloli, ta yadda za a tabbatar da yunkurin raya birane har zuwa dogon lokaci kuma bisa hanyar gaskiya. Domin cim ma wannan manufa, gwamnatin Kenya za ta mai da hankali wajen tsai da mamufofi da dokoki, da kara kwarewarta domin gudanar da harkoki, da yin muhimman gine-gine da yawa. Gwamnatin Kenya kuma za ta sa lura sosai kan matsalar unguwannin da aka gina ba tare da samun yarda daga gwamnati ba, kuma ta riga ta tsai da "shirin kyautata unguwannin talakawa na kasar Kenya" da shirin ba da taimako wajen kudi, an kimanta cewa, cikin shekara 13 masu zuwa za a ware dala biliyan 20 domin gudanar da wannan shiri".

Bisa matsayin kasa mai tasowa mafi girma, da samun saurin ci gaban tattalin arzaki, kasar Sin ita ma tana fuskantar matsalar rashin daidaici wajen samun ci gaba tsakanin kauyuka da birane, kuma tsakanin shiyyoyi daban-daban. Yayin da madam Fu Wenjuan, shugabar kungiyar wakilan kasar Sin, kuma mataimakiyar ministar gine-gine ta kasar ta yi jawabi a gun babban taron ta bayyana cewa, "Domin samun daidaici tsakanin yunkurin raya birane da muhallin albarkatu, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai wajen gudanar da tsarin daidaita da kuma sarrafa ayyukan bunkasa birane, ta tsaya kan manufar samun daidaici wajen bunkasa da tsara fasalin manya da matsakaita da kananan birane da garuruwa. Kyautata sharudan gidajen kwana na mazaunan birane, musamman ma ga wadanda ke samun ramammen kudin shiga, kullum ta zama wata matsalar da ta jawo hankalin gwamnatin kasar Sin sosai." (Umaru)