Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-17 18:47:55    
Sin ta taka rawa mai yakini a kan batun Darfur

cri
Kwanan nan, batun Darfur yana ta daukar hankulan gamayyar kasa da kasa, musamman ma rahotonnin da wasu kafofin yada labarai na kasashen yammaci suka bayar dangane da tsanancewar matsalar jin kai sun jawo wa mutane damuwa. Kwanan baya, mai taimakawa ministan harkokin waje na kasar Sin, Mr.Zhai Jun ya kai ziyara a kasar Sudan a matsayin manzon musamman ma gwamnatin kasar Sin, kuma ya yi bincike kan halin da shiyyar Darfur ke ciki a fannin tsaro da kuma harkokin jin kai. Sabo da haka, wakiliyarmu ta kai masa ziyara, don ku ji ta bakinsa kan hakikanin halin da yankin Darfur ke ciki da matsayin kasar Sin a kan batun Darfur da kuma rawar da take takawa kan batun.

Da zarar wakiliyarmu ta shiga ofishinsa, sai malam Zhai Jun ya yi farin ciki ya gaya mata cewa, "akwai wata bishara, an sami sabon ci gaba a kan batun Darfur." Ashe, kafin zuwan wakiliyarmu, malam Zhai Jun ya gana da jakadan Sudan a Sin, kuma ya sami labarin cewa, Sudan da MDD da kungiyar tarayyar Afirka sun cimma daidaito kan dukan abubuwan da ke cikin shirin Annan na mataki na biyu, wanda kuma ke nufin, an sake samun ci gaba a kan batun Darfur.

A lokacin hirar, malam Zhai Jun ya bayyana cewa, Sin ta yi kokari sosai a wajen sa kaimin daidaita batun Darfur. Ya ce,"Daga ko wane fanni ne, Sin tana iya taka rawa mai yakini, kuma har kullum muna taka irin wannan rawar. Sin zaunanniyar kasa ce da ke cikin kwamitin sulhu, haka kuma kasa ce da ke zumunci da Sudan, ko shakka babu ba ma son ganin kasar da muke zumunci da ita ta gamu da rikici ko tashin hankali ko kuma wasu matsalolin da za su iya lalata bunkasuwarta. Rawar da muke takawa tana da yakini, haka kuma tana da amfani. Mun yi kokari sosai, shugaban kasar Sin shi ma ya yi kokari, a yayin da mai ba da shawara ga shugaban kasar Sudan ya kawo ziyara a kasar Sin, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin, malam Tang Jiaxuan shi ma ya yi shawarwari da shi. A sauran fannoni ma, muna tuntubar sauran kasashe mambobin kwamitin sulhu da MDD da kuma kungiyar tarayyar Afirka."

Bayan haka, malam Zhai Jun yana kuma rike da kyakkyawar fata kan makomar batun Darfur, sakamakon abubuwan da ya gani a shiyyar Darfur. Ya ce,"kwanan nan ba da dadewa ba, na kai ziyara a kasar Sudan, kuma na je shiyyar Darfur, inda na ga sansanonin 'yan gudun hijira uku wadanda ke da girma, kuma ina ganin shiyyar da na tafi suna cikin kwanciyar hankali, ba kamar irin hali mai tsanani a cewar kasashen yammaci ba, gwamnatin Sudan tana iya shawo kan halin. Amma duk da haka, kasancewar sansanonin 'yan gudnn hijira su kansu sun shaida kasancewar matsalar 'yan gudun hijira da kuma matsalar jin kai, amma halin ba shi da tsanani sosai, akwai tabbaci, akwai tsari."

Amma kwanan nan, akwai kalamin da ya bullo dangane da kasar Sin, inda ake ganin cewa, zuba jari a Sudan da hukumomi masu jarin kasar Sin suka yi da kuma fitar da makamai zuwa Sudan da Sin ta yi sun kara hura wutar rikicin Darfur, sabo da haka, ya kamata Sin ta dauki alhakin matsalar jin kai a shiyyar Darfur. Game da wannan, malam Zhai Jun ya ce,"abu maras kan gado ne a ce kamata ya yi Sin ta dauki alhakin batun Darfur. Sabo da na farko, Darfur tana da nisa da mu, ainihin matsalar Darfur shi ne kwace albarkatun kasa da wasu kabilun wurin ke yi, babu maganar Sin ta dauki alhakin gaba daya. Mai yiwuwa ne wasu su ce, Sin tana da kyakkyawar hulda da Sudan, sabo da haka, ya kamata Sin ta dauki alhakin batun Darfur. Gaskiya muna da hulda mai kyau da Sudan, amma irin huldar tana amfana wa juna, wadda kuma ta dace da ka'idoji biyar na zama tare cikin lumana, mun bayar da taimako ga Sudan ne domin taimaka wa Sudan wajen bunkasa da kyautata zaman rayuwar jama'arta. Matsalar Darfur ta kasance rikicin da ke tsakanin dakaru, amma idan jama'a suna iya zaman rayuwarsu yadda ya kamata, kuma tattalin arziki ya sami babban ci gaba, to, matsalar za ta bace. Kamata ya yi a kara ba da taimako ga shiyyar Darfur, ta yadda shiyyar za ta iya samun ci gaba, ta hakan kuma za a iya daidaita matsalar."

Bayan haka, malam Zhai Jun yana kuma ganin cewa, babu wata hujja an ce Sun tana da ruwa da batun makamai na Darfur. Sabo da na farko, Sin tana fitar da makamai kalilan ne ga kasashen waje, na biyu, Sin tana fitar da makamai ne ga kasashe masu mulkin kansu ne kawai, wadanda ke neman tsaron kansu, tana kuma bukatar tabbacinsu (Lubabatu)