Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-17 18:26:35    
Kasar Sin tana fata bangarorin da abin ya shafa za su ci gaba da yin shawarwari domin warware matsalar Darfur yadda ya kamata

cri

A ran 17 ga wata a birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Liu Jianchao ya bayyana cewa, kasar Sin tana fata bangarorin da abin ya shafa za su ci gaba da yin shawarwari domin warware matsalar Darfur yadda ya kamata.

Bisa labarin da muka samu, an ce, kasar Sudan ta riga ta daddale wata hadaddiyar yarjejeniya da MDD da kuma kawancen kasashen Afirka domin girke sojojin kawance a yankin Darfur.

Game da haka, Mr Liu ya ce, kasar Sin tana murna sosai da ganin haka, wannan kuma ya zama muhimmin ci gaba da aka samu a yunkurin warware matsalar Darfur. Hakikanan abubuwa sun shaida cewa, tsarin yin shawarwari da ke tsakanin bangarori 3 cikin daidaici yana da amfani, kuma yana da muhimmiyar ma'ana ga aikin warware matsalar Darfur. A sa'i daya kuma, Mr Liu ya fadi cewa, abu mai muhimmanci ga aikin warware matsalar Darfur shi ne gwamnatin kasar Sudan da jama'arta.(Danladi)