Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-17 16:55:19    
Gidan ibada na lama na Gandan

cri

A cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. Kamar yadda muka saba yi, da farko dai, za mu karanta muku wasu abubuwa kan wani gidan ibada na lama da ke kusa da birnin Lhasa, sunansa gidan ibada na lama na Gandan, daga bisani kuma, sai wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Wurin shakatawa na gandun daji na babban dutsen Songshan na Beijing'

An gina gidan ibada na lama na Gandan a arewa maso gabashin birnin Lhasa na jihar kabilar Zang ta Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, nisan da ke tsakaninsa da Lhasa ya kai misalin kilomita 40. Gidan ibada na lama na Gandan shi ne gidan ibada na lama na farko da masu bin darikar Gelugpa suka gina. Ya zuwa yanzu dai ya kai muhimmin matsayi a cikin addinin Buddha na Tibet.

Marigayi Tsong Kha-pa, wanda aka girmama shi saboda ya kafa darikar Gelugpa shi ne ya gina gidan ibada na lama na Gandan a shekara ta 1409, sa'an nan kuma, ya rigamu gidan gaskiya a nan. Wannan gidan ibada na lama na daya daga cikin manyan gidajen lama 3 na darikar Gelugpa a Lhasa. Saura 2 su ne gidajen ibada na lama na Drepung da Sera.

A cikin dukkan muhimman gidajen lama da ke jihar Tibet, gidan ibada na lama na Gandan ya fi shan wahala a cikin wani lokacin musamman na kasar Sin, wato a tsakanin shekara ta 1966 zuwa ta 1976. A lokacin can, an rushe yawancin gine-ginensa, wadanda suka hada da muhimmin zaure da kushewar marigayi Tsong Kha-pa da aka yi da zinariya da kwalejin nazarin littattafan addini na Jiangtse da kuma na Shartse. Amma gidan ibada na lama na Gandan ya sake samun kyan gani bayan da aka yi masa kwaskwarima duka a shekarun 1990.

Yanzu lama kimanin 500 suna zama a cikin gidan ibada na lama na Gandan, a cikinsu kuma wasu kimanin 200 suna nazarin littattafan addini a cikin kwalejin nazarin littattafan addini na Shartse, sauran kuma suna cikin kwalejin na Jiangtse. A can da wadannan kwalejojin nazarin littattafan addini sun taba nazarin littattafan addini dai-dai. Amma yanzu suna nazarin littattafan addini da kuma tattaunawa kan addinin Buddha na Tibet tare a cikin muhimmin zauren, hakan yana amfana wa hadin kansu sosai. Yawancin lama da ke cikin gidan ibada na lama na Gandan sun zo daga jihar Tibet ne, wasu daga cikinsu kuma sun zo daga lardunan Gansu da Sichuan da Qinghai da sauran wuraren kasar Sin.

Jajayen kushin sun mamaye yawancin muhimmin zauren gidan ibada na lama na Gandan, yayin da aka rataye tutoci da yawa masu launuka daban daban da sha'awa daga silin muhimmin zauren.(Tasallah)