Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-17 16:52:52    
Kila mata sun fi saukin kamuwa da sankarar huhu sakamakon shakar hayakin taba

cri

Bisa sabon binciken da manazarta na kasar Amurka suka gudanar, an ce, mata da suka kamu da sankarar huhu da yawansu ya kai 20 cikin dari ba su shan taba ko kadan, kuma mai yiyuwa ne dalilin da ya sa suka kamu da cutar shi ne sabo da su kan shaki hayakin taba a kullum.

Manazarta na jami'ar Stanford ta kasar Amurka sun bayar da rahoto a kan mujallar ilmin sankara ta kasar da aka buga a ran 9 ga watan Febrairu, inda suka bayyana cewa, sun zabi mutane fiye da miliyan guda da shekarunsu ya kai 40 zuwa 79 da haihuwa a kasashen Amurka da Sweden wajen yin nazari kan yiyuwar kamuwa da sankarar huhu. Kuma abubuwan da aka yi nazari a cikin binciken sun kunshi irin abincin da su kan ci, da yanayin zaman rayuwarsu da kuma cuttuttukan da suka taba kamuwa da su da dai sauransu.

Daga baya kuma kididdigar nazarin ta bayyana cewa, daga cikin matan da ba su shan taba, yawan wadanda suke kamuwa da sankarar huhu a ko wace shekara ya kai 14 zuwa 21 a cikin dubu 100. Kuma daga cikin mazan da ba su shan taba, yawan wadanda suke kamuwa da sankarar huhu ya kai 5 zuwa 14 cikin dubu 100, sabo da haka an gano cewa, matan da ba su shan taba sun fi saukin kamuwa da sankarar huhu. Amma a cikin mutanen da suke shan taba, ko maza ko mata, yiyuwar kamuwa da sankarar huhu gare su ta ninka sau 10 zuwa 30 idan an kwatanta da wadanda ba su shan taba.

Heather Warerly, mai kula da nazarin ya bayyana cewa, an riga an tabbatar da cewa, shakar hayakin taba zi kara hadarin kamuwa da sankarar huhu, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa yawancin mutanen da ba su shan taba da muka ambata a baya suka kamu da sankarar huhu. Bayan da aka yi watsi da sauran hadarurrukan da za su haddasa sankara, Mr. Warerly yana ganin cewa, muhimmin dalilin da ya sa yawancin mata da ba su shan taba su kan kamu da sankarar huhu shi ne shakar hayakin taba, amma ya zuwa yanzu manazarta ba su fahimci ko mene ne dalilin da ya sa shakar hayakin taba ya fi yi wa mata illa idan an kwatanta su da maza?

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan ayyukan koyarwa na kananan kabilun kasar Sin. Kasar Sin wata kasa ce mai yawan kabilu. Ban da kabilar Han, ana iya samun kananan kabilu 55 a cikin kasar. Sabo da dililan zamantakewar al'umma da tarihi da kuma yanayin halittu, shi ya sa matsayin ayyukan koyarwa na wasu yankunan kananan kabilun kasar Sin yana baya baya, kuma bai iya biyan bukatun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar wurin ba. Sabo da haka, a cikin shekaru masu yawa da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta kafa makarantun kabilu iri daban daban, musamman ma makarantu masu ba da ilmi mai zurfi bisa halin da kananan kabilu ke ciki domin horar da kwararru na fannoni daban daban. To a cikin shirinmu na yau, za mu leka wata makaranta daga cikinsu, wato jami'ar kabilu ta kudu maso yammacin kasar Sin.(Kande)