
A ran 16 ga wata a birnin Beijing, an kaddamar da hadaddiyar kungiyar sada zumunci ta kamfanonin 'yan uwa na Taiwan ta duk fadin kasar Sin, wadda ta zama hadaddiyar kungiyar sada zumunci a tsakanin 'yan kasuwa na Taiwan ta farko da aka kafa a babban yankin kasar Sin.
Kungiyoyin kamfanonin 'yan kasuwa na Taiwan da yawansu ya kai 100 da ke cikin jihohi 25 na babban yankin kasar Sin sun kaddamar da wannan hadaddiyar kungiya bisa burinsu ba domin neman samun riba ba.

A gun taron kafa hadaddiyar kungiyar, shugaba na karo na farko na wannan kungiya 'dan kasuwa na Taiwan Mr Zhang Hanwen ya bayyana cewa, bayan da aka kafa kungiyar, za a kara sa kaimi ga yin mu'amala a tsakanin jama'ar gabobin biyu na zirin Taiwan, da kuma sa kaimi ga gabobin biyu da su yi harkokin kasuwanci da aikewa da wasiku da sufuri a tsakaninsu kai tsaye, da kuma sa kaimi ga hadin kai a tsakanin gabobin biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya.
A gun taron kafa hadaddiyar kungiyar, darektan ofishin harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Mr Chen Yunlin ya ce, yana fata kungiyar za ta taimaka wa 'yan kasuwa na Taiwan domin warware matsalolin da suke fuskanta da kuma bayar da amfaninta sosai a tsakanin mambobinta da gwamnati.(Danladi)
|