Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-16 16:46:38    
Manzauna masu fama da talauci na birnin Dalian na kasar Sin sun samu taimakon jiyya

cri

Samar da taimakon jiyya wani muhimmin kashi ne na samar da taimako ga zamantakewar al'ummar kasar Sin. Game da wasu mazaunan birane masu fama da talauci, ba su da kudin ganin likita, kuma ba su shiga inshorar jiyya ba sakamakon dalilai iri daban daban, sabo da haka samun taimakon jiyya shi ne burinsu kurum wajen harkoki lafiyarsu. Birnin Dalian wani birni ne da ke da tashar jiragen ruwa da ke arewa maso gabashin kasar Sin, inda tattalin arizkinsa yake samun ci gaba a gwargwado. Tun shekarar da muke ciki, gwamnatin birnin ta kaddamar da zuba kudade masu yawa domin mazauna masu fama da talauci na birnin za su iya samun taimakon jiyya. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani a kan batun.

Zhang Fengling mai shekaru 51 da haihuwa shi ne wani ma'aikaci na birnin Dalian wanda ba shi da aikin yi yanzu. Yau da shekaru 7 da suka gabata, ya kamu da sankarar jini, kuma domin warkar da shi, an riga an kashe dukkan kudaden da iyalansa suka ajiye da kuma kudaden taimako da abokansa suka samar wadanda yawansu ya kai fiye da yuan dubu 300. Sabo da haka yin wa Zhang Fengling jiyya ya riga ya zama wani nauyi ne da ke bisa wuyan iyalansa. Abu mafi bakin ciki shi ne sabo da rashin kudi, Zhang Fengling bai shiga kofar asibiti domin ganin likita ba a cikin dogon lokaci.

Amma, manufar bayar da taimakon jiyya ga mazauna masu fama da talauci da gwamnatin birnin Dalian ta fitar a shekarar da muke ciki ta samar da dama ga Zhang Fengling wajen warkar da shi. Kuma ya gaya wa wakilinmu cewa,

"A da, idan na bukaci ganin likita, sai kanwata ta tara iyalanmu tare domin tattara kudi. Amma yanzu, gwamnatin Dalian ta ba ni wani kati wajen samun taimakon jiyya wanda ya rage nauyin da ke bisa wuyan iyalansu sosai."

Katin samun taimakon jiyya da Zhang Fengling ya ambta shi ne wata irin takarda da gwamnatin birnin Dalian ta bai wa mazauna masu fama da talauci wajen samun taimako a fannin jiyya. Bisa abubuwan da aka tanada a cikin manufar, an ce, game da dukkan mazaunan birnin wadanda albashinsu bai iya taka kara ya karya ba kuma ba su shiga inshorar jiyya ba, suna iya samun gatancin da gwamnatin birnin ta nuna musu a fannin jiyya, wato ko wanensu ya iya samun yuan 100 a ko wace shekarar wajen ganin likita, haka kuma idan sun kwanta a asibiti, matsakaicin yawan kudaden taimakon jiyya da ko wanensu ya samu ya kai yuan 4300. Ban da wannan kuma domin aiwatar da wannan sabuwar manufar ba da taimakon jiyya, gwamnatin birnin Dalian za ta kebe kudi yuan miliyan 55 a ko wace shekara.

Ya zuwa yanzu, yawan mazaunan birnin da suka samu taimakon jiyya kamar Zhang Fengling ya kai dubu 76. Kuma yawancinsu ba su taba yin ragista wajen neman samun taimakon jiyya ba, har ma wasu daga cikinsu ba su san manufar, sai an ba su irin wannan taimako. Game da wannan, Madam Guo Xiaoxuan, shugabar ofishin kula da harkokin unguwar Malan inda Zhang Fengling ke zama ta bayyana cewa,

"Bayan da muka yi bincike, mun gano cewa, akwai mazauna masu fama da talauci fiye da 1000 a unguwarmu. Kuma game da wandanda ba su shiga inshorar jiyya ba, mun gabatar da sunayensu ga hukumar kula da harkokin fararen hula ta birnin Dalian domin ba su taimakon jiyya. Gwamnatinmu ita kanta ta gudanar da wannan aiki a maimakon haka sun yi ragista wajen neman samun irin wannan taimako."

Bangaren asibitoci na birnin Dalian ya nuna maraba sosai da a aiwatar da manufar samar da taimakon jiyya. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da bayan da aka aiwatar da manufar, an ba da taimako sosai wajen rage matsalolin da ke tsakanin likitoci da masu fama da talauci. Mr. Zhang Zhonglu, mataimakin shugaban asibitin sada zumunta na birnin Dalian ya gaya mana cewa,

"Mu kan gamu da irin wadannan mutane masu fama da talauci, wato idan suka bi hanyoyin ganin likita da a kan bi kullum, lokacin da suke biyan kudi, ko kuma lokacin da suke jira wajen biyan kudi, za su cika da fushi, har ma za su nuna bacin rai ga likitocinmu, kuma wannan shi ne wani muhimmin batu da ke lalata dangankatar da ke tsakanin asibitoci da masu fama da cututtuka. Amma bayan da gwamnatinmu ta aiwatar da wannan kyakkyawar manufar ba da taimako, fararen hula masu fama da talauci da dimbin yawa sun samu taimako daga gwamnatin, ta haka an sassauta rikicin da ke tsakanin asibitoci da masu fama da cututtuka lokacin da muke yin musu jiyya."

Ban da wannan kuma, Mr. Zhang ya bayyana cewa, a karkashin jagorancin gwmanatin Dalian, asibitocin birnin sun fitar da manufofi a jere wajen nuna wa masu fama da talauci gatanci. Alal misali, game da masu fama da talauci, lokacin da ake yi musu muhimmin binciken lafiya da kuma tiyata, za a rage kashi 30 bisa dari na kudaden da suka kashe wajen ganin likita.(Kande Gao)