'Yan kabilar Sala suna zama a yankunan da ke iyaka tsakanin tudun Qinghai-Tibet da sauran wuraren kasar Sin, wato yawancinsu suna zama a gundumar Xunhau ta kabilar Sala mai cin gashin kanta da gundumar Huilong ta kabilar Hui mai cin gashin kanta da sauran gundumomi da birane na lardin Qinghai da wasu kauyuka a lardin Gansu da jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000 a duk fadin kasar Sin, yawan mutanen kabilar ya kai kimanin dubu 104. Suna amfani da yaren Salad a harsunan Sinanci da Tibet.
Kafin shekarar 1949, 'yan kabilar Sala suna dogara da kansu wajen raya tattalin arziki, suna cikin zaman al'ummar mulkin kama karya, suna kuma cikin mawuyacin hali kwarai.
Bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin, an yi gyare-gyare kan zaman al'ummarsu ta hanyar dimokuradiyya, an kwace ikon musamman daga hannun masu hannu da shuni na kabilar. Monama sun samu gonakin da suke bukata. A waje daya kuma, an kafa gwamnatin mai cin gashin kanta a yankunan 'yan kabilar Sala. Sakamakon haka, 'yan kabilar Sala sun fara samun cigaga wajen raya harkokin tattalin arziki da zaman al'umma yadda ya kamata, zaman rayuwarsu ma ya samu kyautatuwa sosai. Yanzu, kabilar Sala tana da jami'ai da masana da kwararru iri iri. Sun kuma sami cigaba sosai a fannonin al'adu da ilmi da kiwon lafiya da makamatansu.
Kabilar Sala tana da al'adunta na musamman, suna yada adabi da al'adunsu da baki. Adabinta yana kunshe da tatsuniyoyi da almara da Karin magana da kacici-kacici da dai sauransu. A waje daya kuma 'yan kabilar Sala sun kware kan rera wakoki iri iri ciki har da wakokin liyafa da na furanni da na Sala. Wakokin Sala wakoki ne da 'yan kabilar Sala suke rerawa da yarensu domin bayyana tunaninsu. Wakokin liyafa wakokin gargajiya ne da suke rerawa a gun bukukuwan aure.
Bisa al'adar kabilar Sala, kowane saurayi yana iya auren mace daya. Iyaye ne suke nema wa yaransu aure. Lokacin da ake shirya bikin aure, imam ne yake shugabantar bikin.
A waje daya kuma, 'yan kabilar Sala suna cin abincin da aka yi da garin alkama da dankali da ganye iri iri da naman rogo da na kaza da na shannu, kuma suna shan madara da ti irin da ake yi da alkama.
'Yan kabilar Sala suna bin addinin Musulunci. Yawancinsu suna cikin darikar Sunni. Sabo da haka, suna azumi, kuma suna murnar bikin babbar salla da bikin karamar salla. (Sanusi Chen)
|