Bayan da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya gama ziyarar aiki a kasar Japan a ran 13 ga wata, ya tashi daga birnin Osaka domin komowa gida.
Wannan shi ne karo na farko da firayim ministan kasar Sin ya kai wa kasar Japan ziyara bayan shekaru 7 da suka gabata.
Kafin Wen Jiabao ya bar birnin Osaka a ran 13 ga wata, ya yi bayani a gaban kafofin watsa labarai, cewa wannan ziyararsa a kasar Japan ta ci nasara sosai. A lokacin ziyararsa, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Japan Abe Shinzo, inda bangarorin biyu suka samu ra'ayi daya kan al'amura masu yawa, musamman ma a kan batun kafa dangantakar moriyar juna tsakanin kasashen Sin da Japan bisa manyan tsare-tsare. Kuma yana ganin cewa, mutanen sassa daban daban na kasar Japan suna nuna sahihanci wajen ci gaba da raya dangantakar aminci tsakanin kasashen biyu.(Kande Gao)
|