Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-13 14:16:12    
Jam'iyyun siyasa na kasar Japan sun yaba wa jawabin Wen Jiabao

cri

Bisa labarin da jaridar Asahi Shimbun ta kasar Japan ta bayar a ran 13 ga wata, an ce, jam'iyyun siysa daban daban na kasar Japan sun yaba wa jawabin da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi a ran 12 ga wata da safe a majalisar dokokin kasar Japan.

Babban sakataren majalisar ministocin kasar Japan Shiozaki Yasuhisa yana ganin cewa, jawabin Wen ya bayar da ra'ayoyi masu yakini da yawa. Wakilin Jam'iyyar Komei wadda ta zama daya daga cikin jam'iyyun da ke rike da ragamar mulkin Japan Mr Ota Akihiro ya fadi cewa, a fili ne, jawabin da Mr Wen ya bayar ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Sin da Japan su hanga nan gaba.

Jaridar Asahi ta ci gaba da cewa, a yayin da ya tabo magana a kan batun tarihi, Mr Wen ya bukaci Japan ta dauki hakikakan matakai domin nuna ra'ayinta a kan batun tarihi. Game da haka, babban sakataren jam'iyyar 'yanci da dimokuradiyya ta kasar Japan mai kula da harkokin majalisar ministoci Nikai Toshihiro ya ce, masu kai hari sun manta, amma masu shan hari ba su manta ba, kamata ya yi kasar Japan ta rike da wannan a zuci a ko wane lokaci. Mr Hatoyama Yukio, darektan jam'iyyar dimukuradiyya ta kasar Japan, wadda ba ta rike da ragamar mulkin Japan ba ya bayyana cewa, ya zama wajibi ne gwamnatin kasar Japan ta yi la'akari sosai a kan jawabin Wen Jiabao, kuma ta dauki mataki domin amsa shi.(Danladi)