Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-13 14:13:10    
Firayin ministocin Sin da Japan sun halarci taron taya murnar cikon shekaru 35 da komawar dangantakar Sin da Japan yadda ya kamata

cri

A ran 12 ga wata, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao da takwaransa na kasar Japan Abe Shinzo sun halarci taron taya murnar cikon shekaru 35 da maido da dangantaka tsakanin Sin da Japan yadda ya kamata, kuma sun halarci bikin bude shagalin shekarar yin mu'amala a tsakanin Sin da Japan a fannonin al'adu da wasanni.

Mr Wen ya ce, kyautattuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Jaopan da kuma bunkasuwarta ya dogara ga kokarin da gwamnatocin biyu suke yi, kuma ya dogara ga ra'ayin 'yan siyasa, amma tushen sada zumunci a tsakanin kasashen biyu yana kasancewa a zuciyar jama'ar kasashen biyu, zumuncin da ke cikin zukatansu shi ne zumunci mai dorewa. Mr Abe ya bayyana cewa, shi da Mr Wen sun samu muhimmin ra'ayi daya a fannoni da yawa, wannan ya nuna cewa, kasashen biyu su samu sabon ci gaba wajen raya dangantakarsu irin ta moriyar juna bisa manyan tsare tsare, shi da kansa zai kokarta sosai domin kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakarsu.

Domin taya murnar cikon shekaru 35 da komawar dangantakar Sin da Japan yadda ya kamata, gwamnatocin kasashen biyu sun yanke shawarar shirya shagalin shekarar yin mu'amala a tsakanin Sin da Japan a fannonin al'adu da wasanni, Mr Wen da Abe sun halarci bikin bude shagalin.(Danladi)