Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-12 20:21:39    
Kasar Sin tana kara mai da hankali ga ayyukan mayar da wasu sunayen kakayyakin tarihi da za su zama na duniya

cri

Kwanan nan ba da dadewa ba, hukumar kula da harkokin kayayyakin tarihi ta kasar Sin ta sake shirya sunayen kayayyakin tarihi da za su zama na duniya da kuma kara mai da hankali ga kula da harkokin shigar da sunayensu. Idan ba a kiyaye kayayyakin tarihi da za a shirya su don su zama na duniya sosai ba, to za a yi watsi da wadannan sunayen kayayyakin tarihi, wato za su rasa cancantar ikonsu na neman shiga cikin sunayen kayayyakin tarihi na duniya.

Kasar Sin ta shiga cikin yarjejeniyar kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu da na halittu na duniya a shekarar 1985, ya zuwa yanzu, yawan kayayyakin tarihi na kasar Sin da suka riga suka zama kayayyakin tarihi na duniya ya kai 31. Bisa ka'idojin da aka tsara a cikin yarjejeniyar, an bayyana cewa, mayar da sunayen kayayyakin tarihi da aka shirya su don su zama na duniya cikin sunayen kayayyakin tarihi na al'adu da na halittu na duniya na hukumar Unesco ta Majalisar dinkin Duniya ya zama sharadin farko ga neman shiga cikin jerin sunayen kayayyakin tarihi na duniya. A shekarar 1996, karo na farko ne kasar Sin ta gabatar wa hukumar Unesco ta Majalisar Dinkin Duniya sunayen kayayyakin tarihi da aka shirya su don su zama na duniya na rukunin farko, Bisa abubuwan da hukumar Unesco ta tsaida, an ce, a kalla dai za a gyara sunayen nan a karo daya a cikin shekaru goma goma.

Saboda haka, ba da dadewa ba, hukumar kula da harkokin kayayyakin tarihi ta kasar Sin ta zabi kayayyakin tarihi da yawansu ya kai 35 daga cikin 129 da wurare daban daban na kasar Sin suka yi rokon mayar da su don su zama na duniaya da kuma sake tabbatar da sabbin sunayen kayayyakin tarihi don su zama na duniya. Mataimakin shugaban hukuamr kula da kayayyakin tarihi na kasar Sin Mr Tong Mingkang ya bayyana cewa, game da sake shirya sunayen kayayyakin tarihi , da farko a aiwatar da yarjejeniyoyin kasashen duniya, na biyu, samun sharadin kara habakawa da yin sauye-sauyen ra'ayoyi kan kayayyakin tarihi. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, a kasashen duniya, ana kara habaka abubuwa ga kayayyakin tarihi da kuma yada su, wato an haifar da tafarkin al'adu da kayayyakin tarihi na masana'antu da sauran sabbin ra'ayoyi kan kayayyakin tarihi da sabbin samfurorinsu, kuma za a ci gaba da habaka su, saboda haka ana neman kasar Sin da ta sake tabbatar da sunayen kayayyakin tarihi da za a mayar da su don su zama na duniya.

Amma rokon da gwamnatocin wurare daban daban na kasar Sin suka yi na neman shigar da kayayyakinsu na tarihi cikin sunayen kayayyakin tarihi na duniya bai ci nasara ba, wani mashahurin kwararren kasar Sin wajen kiyaye kayayyakin tarihi na duniya Mr Guo Zhan ya bayyana cewa, aikin da muke yi na biyan bukatun mayar da sunayen kayayyakin tarihi da muka shirya don su zama na duniya ya yi daidai da matsayin mayar da kayayyakin tarihi don su zama na duniya. Wannan kwararren ya kuma bayyana cewa, tun daga shekaru 80 na karnin da ya wuce, a kowace shekara, kungiyar Unesco tana mayar da kayayyakin tarihi na al'adu da na halittu na kasar Sin don su zama na duniya , wannan ya ba da taimako mai yakini ga sanar da sunayen wadannan kayayyakin tarihi ga duniya.

Wani shugaban sashen kiyaye kayayyakin tarihi na hukumar kiyaye kayayyakin tarihi ta kasar Sin mai suna Gu Yucai ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, a wajen kiyaye kayayyakin tarihi, kasar Sin tana kusancin matsayin kasashen duniya , kuma tana yin ma'amala da yawa da sauran kasashe. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, mun yi kokarin nazari kan hanyoyin da za mu bi don dace da halayen musamman na kasar Sin na kiyaye kayayyakin tarihi da dai sauransu.(Halima)