Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-12 18:22:03    
Firayim ministan kasar Sin ya ba da jawabi a majalisar dokokin kasar Japan

cri
Ran 12 ga wata da safe, firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin da ke ziyara a kasar Japan ya yi jawabi mai lakabi haka 'Domin zumunci da hadin gwiwa' a gun majalisar dokoki ta Japan, ta haka ya zama kusan kasar Sin ne na farko da ya yi jawabi a gun majalisar dokoki ta Japan a cikin shekaru 22 da suka wuce.

A cikin jawabinsa, Mr. Wen ya nuna cewa, yau da shekaru 35 da kasashen Sin da Japan suka komar da dangantakar da ke tsakaninsu yadda ya kamata, kasashen 2 sun sami babban ci gaba wajen raya huldarsu, jama'arsu kuma sun ci gajiya sosai. Hada kai a tsakanin Sin da Japan zai kawo musu alheri, amma yin gwagwarmaya a tsakaninsu zai kawo musu illa, tabbatar da sada zumunta a tsakanin zuriyoyinsu yana dacewa da ci gaban tarihi da kuma burin jama'arsu duka, haka kuma buri ne na kasashen Asiya da gamayyar kasashen duniya.

Ya kara da cewa, a matsayinsu na muhimman kasashe na Asiya da na duniya, huldar da ke tsakanin Sin da Japan ta ba da babban tasiri kan Asiya har ma duk duniya, shi ya sa kamata ya yi kasashen 2 su kara taimakon juna da hada kansu, su kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabashin Asiya tare, da kuma sa kaimi kan hadin gwiwa a tsakanin kasashen yankin da suke ciki da himmantuwa kan farfado da Asiya.

Bayan da ya yi jawabi, Mr. Wen ya gana da shugaban majalisar wakilai ta Japan Youhei Kono da shugabar majalisar dattijai ta Japan madam Chikage Ogi daya bayan daya.

Daga baya sarkin Japan Akihito ya gana da shi a fadar sarkin.

A wannan rana kuma, firayim minista Wen da takwaransa na Japan Shinzo Abe sun halarci da kuma shugabanci taron kaddamar da tsarin yin tattaunawa a tsakanin manyan jami'an harkokin tattalin arzki na Sin da Japan.

A ran nan da dare, Mr. Wen ya gana da wasu shugabannin jam'iyyun Japan daya bayan daya.(Tasallah)