Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-12 17:30:51    
Firayin ministan kasar Sin ya bayar da jawabi a gun majalisar wakilai ta kasar Japan

cri

A ran 12 ga wata, wato Yau, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Japan ya bayar da wani jawabi a majalisar wakilai ta kasar Japan. Taken jawabinsa shi ne "Domin sada zumunta da hadin guiwa". Wannan ne karo na farko da firayin ministan kasar Sin ya bayar da jawabi a gun majalisar dokokin kasar Japan a cikin shekaru 22 da suka wuce. Yanzu ga wani bayanin da wakilanmu suka aiko mana daga Japan.

"Yau, ina farin ciki sosai domin samun damar bayar da jawabi a majalisar dokokin kasarku da ganawa da 'yan majalisun dattawa da wakilai na kasarku. Tare da fatan alheri da gaisuwa mai dimbin yawa, ina fatan ku tare da dukkan jama'ar kasarku kuna nan lafiya. Kuma ina nuna godiya da girmamawa ga dukkan abokan kasarku wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan.", a cewar Wen Jiabao.

Firayin minista Shinzo Abe da ministan harkokin waje Taro Aso na kasar Japan sun kuma saurari jawabin da Wen Jiabao ya bayar. A cikin jawabinsa, Mr. Wen ya bayyana cewa, bangarorin kasashen biyu suna bukatar gado da raya zumuncin da ya dade yake kasancewa a tsakanin Sin da Japan domin sada zumunta da hadin guiwa a tsakaninsu. A waje daya kuma, Mr. Wen ya nuna cewa, bangarorin biyu suna bukatar yin nazari da koyon darusan da aka yi a cikin tarihi. Hare-haren da kasar Japan ta kawo wa kasar Sin a cikin tarihi sun kawo illa sosai ga Sinawa tare da kuma jama'ar Japan. Mr. Wen ya ce, "Jaddada yin amfani da tarihi domin hango gaba ne, amma ba domin tunawa da kiyayya ba. Tun daga aka komar da dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Japan yadda ya kamata, gwamnati da shugabanni na kasar Japan sun riga sun bayyana matsayinsu har sau da yawa kan batun tarihi. A fili ne sun amince da hare-haren da kasar Japan ta taba yi, kuma sun nemi gafara. Sabo da haka, gwamnati da jama'ar Sin sun nuna musu yabo kwarai. A sahihanci ne muna fatan bangaren Japan zai dauki hakikanan matakan cimma alkawuransu. Idan kasashen Sin da Japan suka zama tare cikin lumana, wannan zai moriyarsu juna, amma idan su yi adawa da juna, shi ke nan, dukkansu za su ci hasara."

Mr. Wen Jiabao ya bayyana cewa, A cikin sabon halin da ake ciki yanzu, ya kasance da kwatakwacin moriya da yawa a tsakanin Sin da Japan, suna kuma fuskantar manyan batutuwan da ya kamata kasashen biyu su daidaita su tare. Makasudin kafa dangantakar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu shi ne bin ka'idar tarihi da zuciyar jama'a. Haka kuma, Mr.Wen ya bayar da ka'idoji 5 da ya kamata bangarorin biyu wato Sin da Japan su bi su tare domin kai wa dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan wani sabon mataki da cimma burin zaman tare cikin lumana da sada zumunta a tsakanin zuriyoyi na nan gaba da moriyar juna da kuma neman cigaba tare. Da farko dai, Mr. Wen ya ce, ya kamata a kara amincewa da juna da cimma alkawuran da aka yi. Ya ce, "Takardun siyasa 3 ciki har da 'Hadaddiyar Takarda da kasashen Sin da Japan suka bayar tare" sun amince da hakikanan abubuwan da suka faru a da, kuma sun tsara makomar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta fuskokin siyasa da dokoki. Wadannan takardu 3 tushe ne ga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Idan bangarorin 2 suka bi dukkan ka'idojin da aka tsara a cikin wadannan takardun siyasa 3 a koda yaushe, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu za ta samu cigaba lami lafiya."

Bugu da kari kuma, a cikin jawabinsa, Mr. Wen ya sake bayyana matsayin bin hanyar zaman lafiya wajen neman bunkasuwarta da kasar Sin take dauka. Ya jaddada cewa, "A kullum kasar Sin tana bin hanyar zaman lafiya, amma ba hanyar nuna karfin tuwo ba lokacin da take daidaita batutuwa iri daban daban. Tana kuma cika alkawuran da ta dauka da neman sulhu a tsakaninta da makwabtanta. A nan a zahiri ne na gaya muku cewa, kasar Sin za ta ci gaba da daga tutar shimfida zaman lafiya da neman bunkasuwa da hadin guiwa a tsakaninta da sauran kasashen duniya domin bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana da sauke niyyar raya wata duniya mai jituwa. Ba za mu canja wannan matsayinmu har abada."

Mr. Houhei Kono da madam Chikage Ogi, shugabannin majalisun dattawa da dokoki na kasar Japan sun kuma bayar da jawabai, inda suka nuna cewa, ziyarar da Mr. Wen ke yi tana da muhimmiyar ma'ana wajen kara ciyar da dangantakar sada zumunta irin ta hadin guiwa da ke kasancewa a tsakanin Japan da Sin gaba. (Sanusi Chen)